Pular para o conteúdo
Publicidade

Mika 3

An Tsawata wa Shugabanni da Annabawa

1 Sa’an nan na ce,

"Ku kasa kunne, ku shugabannin Yaƙub,

ku masu mulkin gidan Isra’ila.

Ya kamata ku san shari’a,

2 ku da kuke ƙin abu mai kyau kuke ƙaunar mugunta,

ku da kuke feɗe mutanena

kuke tuge nama daga ƙasusuwansu;

3 ku da kuke cin naman mutanena,

ku feɗe fatar jikinsu

kuke kakkarya ƙasusuwansu,

kuke yayyanka su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a toya,

kamar naman da za a sa a dafa."

4 Sa’an nan za su kira ga Ubangiji,

amma ba zai amsa musu ba.

A wannan lokaci zai ɓoye fuskarsa daga gare su

saboda irin muguntar da suka yi.

5 Ga abin da Ubangiji ya faɗa,

"Game da annabawa

masu ɓad da mutanena,

in wani ya ciyar da su,

sai su ce akwai salama

amma in bai ciyar da su ba,

a shirye suke su kai masa hari.

6 Saboda haka dare yana zuwa a bisanku, ba tare da wahayi ba,

kuma duhu, ba tare da duba ba.

Rana za fāɗi wa annabawa,

yini kuma zai zama musu duhu.

7 Masu gani za su ji kunya,

masu duba kuma za su ji taƙaici.

Dukansu za su rufe fuskokinsu

gama ba amsa daga Allah."

8 Amma game da ni, ina cike da iko

ta wurin Ruhun Ubangiji

da kuma adalci da ƙarfi,

don a sanar da Yaƙub laifofinsa,

ga Isra’ila kuma zunubinsa.

9 Ku ji wannan, ku shugabannin gidan Yaƙub,

ku masu mulkin gidan Isra’ila,

ku da kuke ƙyamar gaskiya,

kuka karkatar duk abin da yake na gaskiya;

10 kuka gina Sihiyona ta wurin zub da jini,

Urushalima kuma ta wurin mugunta.

11 Hukunce-hukuncen shugabannin ƙasar na cin hanci ne,

firistocinta kuma suna koyarwa don a biya su,

annabawanta kuwa suna yin annabci don neman kuɗi.

Duk da haka suna jingina a kan Ubangiji suna cewa,

"Ba Ubangiji yana tare da mu ba?

Ba bala’in da zai zo mana."

12 Don haka, saboda ku,

za a nome Sihiyona kamar gona,

Urushalima kuma ta zama tarin juji,

tudun haikali kuwa zai zama kurmin ƙayayyuwa.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também