Pular para o conteúdo
Publicidade

Amor próprio

Por Bíblia Online

O amor próprio saudável reconhece o valor que Deus nos deu. Fomos criados à imagem de Deus, maravilhosamente formados. Aceitar-se é honrar o Criador.

Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;

ayyukanka suna da banmamaki,

na san da haka sosai.

Tunaninka suna da daraja gare ni, ya Allah!

Yawansu ba su da iyaka!

A ce zan iya ƙirgansu,

za su fi yashin teku yawa.

Sa’ad da na farka, ina nan tare da kai har yanzu.

Sa’ad da na dubi sammai,

aikin yatsotsinka,

wata da taurari

waɗanda ka ajiye a wurarensu,

wane ne mutum da kake tunawa da shi,

ɗan mutum da kake lura da shi?

Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah

ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.

Yakan da matalauta daga ƙura

yakan ɗaga mabukata daga tarin toka;

ya zaunar da su tare da sarakuna,

tare da sarakunan mutanensu.

Amma Ubangiji ya ce wa Sama’ila, "Kada ka dubi kyan tsarinsa ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai daga waje, amma Ubangiji yakan dubi zuciya."

Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.

Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba. Tabbatacce, gashin kanku ɗin nan ma, an ƙidaya su duka. Kada ku ji tsoro. Darajarku ta fi na kanari masu yawa girma.

Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa.

Seja o primeiro