Pular para o conteúdo
Publicidade

Obadiya 1

1 Wahayin Obadiya.

Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce a kan Edom.

Mun ji saƙo daga wurin Ubangiji cewa,

An aiki jakada zuwa ga al’ummai faɗa musu cewa,

"Ku tashi, mu tafi mu yi yaƙi da ita."

2 "Duba, zan maishe ki ƙarama a cikin al’ummai;

za a rena ki ƙwarai.

3 Fariyar zuciyarki ta yaudare ki,

ke da kike zama can bisa duwatsu1.3 Ko kuwa na Sela

kika kuma yi gidanki a kan ƙwanƙoli,

ke da kike ce wa kanki,

Wa zai iya saukar da ni ƙasa?

4 Ko da yake kina firiya kamar gaggafa

kin kuma yi sheƙarki a can cikin taurari,

daga can zan saukar da ke,"

in ji Ubangiji.

5 "In ɓarayi suka zo miki,

in kuma yan fashi suka shigo gidan da dare,

kash, bala’i zai jira ki

ba abin da suke so ne kawai za su sata ba?

In kuma masu tsinka ya’yan inabi suka zo miki,

ba sukan bar ya’yan inabi kaɗan ba?

6 Amma za a washe Isuwa ƙaƙaf,

a kuma yaye ɓoyayyiyar dukiyarsa!

7 Dukan waɗanda kike tarayya da su, za su kore ki zuwa iyaka;

abokanki kuma za su yaudare ki, su kuma sha ƙarfinki;

waɗanda suke cin abincinki, za su sa miki tarko,1.7 Ma’anar Ibraniyanci don wannan babu tabbas.

amma ba za ki gane ba.

8 "A wannan rana," in jin Ubangiji,

"zan hallaka masu hikimar Edom,

zan shafe mutane masu fahima a duwatsun Isuwa.

9 Jarumawanki, ya Teman, za su razana,

za a kashe kowane mutum a duwatsun Isuwa.

10 Saboda halin kama-karyar da kika yi wa ɗan’uwanka Yaƙub,

za ki sha kunya;

za a hallaka ki har abada.

11 A ranan nan kin tsaya kawai kina zuba ido

yayinda baƙi suke washe dukiyar ɗan’uwanki,

baƙi kuma suka shiga ta ƙofofinsa

suka jefa ƙuri’a don a rarraba Urushalima,

kin tsaya kina kallo kamar ɗaya daga cikin abokan gābansa.

12 Bai kamata ki rena ɗan’uwanki

a ranar masifarsa ba,

ko ki yi farin ciki a kan mutanen Yahuda

a ranar hallakarsu,

ko ki yi fariya sosai

a ranar wahalarsu.

13 Bai kamata ki bi ta ƙofofin mutanena

a ranar bala’insu ba,

ko ki rena su a cikin masifarsu

a ranar bala’insu,

ko ki ƙwace dukiyarsu

a ranar bala’insu ba.

14 Bai kamata ki tsaya a mararraba

don ki kashe waɗanda suke ƙoƙarin tserewa ba,

ko ki ba da waɗanda suka tsere ga hannun maƙiyansu

a ranar wahalarsu ba.

15 "Ranar Ubangiji ta yi kusa

don dukan al’ummai.

Kamar yadda kuka yi, haka za a yi muku;

ayyukanku za su koma a kanku.

16 Kamar yadda kuka sha a kan tuduna mai tsarki,

haka dukan al’ummai za su yi ta sha,

za su sha, su kuma sha

su zama sai ka ce ba su taɓa kasancewa ba.

17 Amma a kan Dutsen Sihiyona za a sami ceto;

Dutsen zai zama mai tsarki,

gidan Yaƙub kuma

zai mallaki gādonsa.

18 Gidan Yaƙub zai zama kamar wuta,

gidan Yusuf kuma kamar harshen wuta;

gidan Isuwa zai zama kamar tattaka,

za a kuma sa masa wuta ƙone.

Babu wanda zai tsira

daga gidan Isuwa."

Ni Ubangiji na faɗa.

19 Mutane daga Negeb za su mamaye

duwatsun Isuwa,

mutane kuma daga gindin tuddai za su mallaki

ƙasar Filistiyawa.

Za su mamaye filayen Efraim da Samariya,

Benyamin kuwa zai mallaki Gileyad.

20 Wannan ƙungiyar Isra’ilawan da aka kwashe zuwa bauta da suke a Kan’ana

za su mallaki ƙasar har zuwa Zarefat;

waɗannan da aka kwashe zuwa bauta daga Urushalima da suke a Sefarad

za su mallaki garuruwan Negeb.

21 Masu kawo ceto za su haura zuwa1.21 Ko kuwa daga Dutsen Sihiyona

don su yi mulkin duwatsun Isuwa.

Ubangiji ne zai yi mulki.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também

Obadias
Ver todos os capítulos de Obadias