Ânimo
O ânimo vem de Deus. Ele nos fortalece, nos encoraja e renova nossas forças. Quando o desânimo chega, as promessas de Deus nos levantam e nos impulsionam a seguir em frente.
Ubangiji ne haskena da cetona,
wa zan ji tsoro?
Ubangiji ne mafakar raina,
wane ne zan ji tsoro?
Ceton adalai kan zo daga Ubangiji;
shi ne mafaka a lokacin wahala.
Sa’ad da na kira, ka amsa mini;
ka sa na zama mai ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa ni.
Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu.
Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.
Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.
Sai mutanen suka amsa suka ce, "Allah ya kiyashe mu da rabuwa da Ubangiji Allahnmu, har a ce mu bauta wa waɗansu alloli! Ubangiji Allahnmu ne da kansa ya fitar da iyayenmu daga Masar, daga ƙasar bauta, ya yi manyan abubuwan al’ajabi, a idanunmu. Ya kiyaye mu cikin dukan hanyar da muka bi, da cikin ƙasashen da muka ratsa;
A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri.
Ina marmarin ganinku don in ba ku wata baiwar ruhaniya, don ku yi ƙarfi wato, don ni da ku mu ƙarfafa juna ta wurin bangaskiyarmu.
Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana.
Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.
Saboda haka ’yan’uwa, cikin dukan damuwarmu da tsananinmu an ƙarfafa mu game da ku saboda bangaskiyarku.