Publicidade

1 Tessalonicenses 5

1 To, yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku, 2 gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za zo kamar ɓarawo da dare. 3 Yayinda mutane suke cewa, "Akwai salama da zaman lafiya," hallaka za auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.

4 Amma ku, yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za zo muku ba zato kamar ɓarawo. 5 Dukanku ya’yan haske ne da kuma ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne. 6 Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai. 7 Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa. 8 Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano. 9 Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi. 10 Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi. 11 Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.

Umarnai na ƙarshe

12 To, muna roƙonku, yan’uwa, ku girmama waɗanda suke aiki sosai a cikinku, waɗanda suke bisanku cikin Ubangiji da kuma waɗanda suke yin muku gargaɗi. 13 Ku riƙe su da mutunci sosai cikin ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna. 14 Muna kuma gargaɗe ku, yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa. 15 Ku tabbata cewa kada kowa rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.

16 Ku riƙa farin ciki kullum; 17 ku ci gaba da yin addu’a; 18 ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.

19 Kada ku danne aikin Ruhu. 20 Kada ku rena annabci, 21 amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau, 22 ku ƙi kowace mugunta.

23 Bari Allah da kansa, Allah na salama, tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 24 Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.

25 Yan’uwa, ku yi mana addu’a.

26 Ku gaggai da dukan yan’uwa da sumba mai tsarki.

27 Na gama ku da Ubangiji ku sa a karanta wannan wasiƙa ga dukan yan’uwa.

28 Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi kasance tare da ku.

Veja também

Publicidade
1 Tessalonicenses
Ver todos os capítulos de 1 Tessalonicenses
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-29_22-07-56-