Pular para o conteúdo
Publicidade

Nahum 2

Ninebe za fāɗi

1 Mai hari yana matsowa a kanki, Ninebe.

Ki tsare mafaka,

ki yi gadin hanya

ki sha ɗamara

ki tattaro dukan ƙarfinki!

2 Ubangiji zai maido da darajar Yaƙub,

kamar ta Isra’ila,

ko da yake masu washewa sun washe su

suka kuma lalatar da inabinsu.

3 Garkuwoyin sojojinsa ja wur ne;

jarumawansa suna sanye da kaya masu ruwan jan garura.

Ƙarafan kekunan yaƙi suna walƙiya

a ranar da aka shirya su;

ana kaɗa māsu da bantsoro.2.3 Da Ibraniyanci; Seftuwajin da Siriyak / mahayan dawakai suna kai da kawowa

4 Kekunan yaƙi sun zabura a tituna,

suna kai da kawowa a dandali.

Suna walƙiya kamar tocila

suna sheƙawa a guje kamar walƙiya.

5 Ninebe ta tattara rundunarta,

duk da haka sun yi ta tuntuɓe a kan hanyarsu.

Sun ruga zuwa katangan birnin,

sun sanya garkuwar kāriya a inda ya kamata.

6 An buɗe ƙofofin rafuffukan

sai wurin ya rurrushe.

7 An umarta2.7 Ma’anar kalmar da Ibraniyanci babu tabbas. cewa birnin

za tafi bauta, za a kuma yi gaba da su.

Bayi yan mata suna kuka kamar tattabaru

suna buga ƙirjinsu.

8 Ninebe tana kama da tafki,

wanda ruwanta yana yoyo.

Suna kuka suna cewa, "Ku tsaya! Ku tsaya,"

amma ba wanda ya waiga.

9 A washe azurfa;

a washe zinariya;

dukiyarsu ba ta da iyaka,

arzikinsu kuma ba ya ƙarewa.

10 Ta zama wofi, an washe ta, an tuɓe ta!

Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa,

jikuna suna rawa, fuskoki duk sun kwantsare!

11 Ina kogon zakokin nan yake yanzu,

inda suka ciyar da ya’yansu,

inda zaki da zakanya sukan shiga,

da ya’yansu, ba mai damunsu

12 Zaki ya kashe abin da ya ishe ya’yansa

ya kuma murɗe wuyan dabbobi

ya cika wurin zamansa da abin da ya kama

ya cika kogwanninsa da abin da ya kashe.

13 "Ina gāba da ke,"

in ji Ubangiji Maɗaukaki.

"Zan ƙone kekunan yaƙinki,

takobi kuma zai fafare ya’yan zakokinki.

Ba kuma zan bar miki namun jejin da za ki kashe a duniya ba.

Ba kuwa za a ƙara jin

muryar yan saƙonki ba."

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também

Naum
Ver todos os capítulos de Naum