Publicidade

Anjos

Por Bíblia Online

Os anjos são seres celestiais criados por Deus para servir, adorar e executar seus propósitos. A Bíblia revela anjos mensageiros, guerreiros e protetores ao longo de toda a história redentora.

Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, "Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne.

Mala’ikan ya ce wa matan, "Kada ku ji tsoro, domin na san cewa kuna neman Yesu wanda aka gicciye ne. Ai, ba ya nan, ya tashi kamar yadda ya faɗa. Ku zo ku ga inda ya kwanta.

Kuna tsammani ba zan iya kira Ubana, nan take kuwa aiko mini fiye da rundunar mala’iku goma sha biyu ba?

Amma mala’ikan ya ce mata, "Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah. Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu.

Amma mala’ikan ya ce musu, "Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane.

"Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama,

a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu."

Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban mala’ikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba."

Suna zuba ido a bisa, zuwa cikin sararin sama yayinda yake tafiya, nan da nan, sai ga mutane biyu saye da fararen riguna tsaye kusa da su. Sai suka ce, "Mutanen Galili, don me kuke tsaye a nan kuna duban sararin sama? Wannan Yesu, wanda aka ɗauke daga gare ku zuwa sama, zai komo daidai yadda kuka ga ya tafi sama."

Gargaɗin ƙarshe

Ku ci gaba da ƙaunar juna kamar yan’uwa. Kada ku manta da yin alheri ga baƙi, gama ta yin haka ne waɗansu suka yi wa mala’iku hidima, ba da saninsu ba.

Ƙauna

In ina iya yin magana da harsunan mutane, da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama kamar kuge mai yawan ƙara, ko kuma ƙararrawa mai amo kawai.

Ba shakka, asirin addini da girma yake.

Ya bayyana cikin jiki,

Ruhu ya nuna shi adali ne,

mala’iku suka gan shi,

aka yi wa’azinsa cikin al’ummai,

aka gaskata shi a duniya,

aka ɗauke shi sama cikin ɗaukaka.

Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada.

Wanda ya ci nasara, kamar su, za a sanya masa fararen tufafi. Ba zan taɓa share sunansa daga cikin littafin rai ba, sai dai zan shaida sunansa a gaban Ubana da mala’ikunsa.

Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

Seja o primeiro
Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-29_22-07-56-