Publicidade

Isaías 15

Annabci a kan Mowab

1 Abin da Allah ya yi magana a kan Mowab shi ne,

An lalatar da Ar a Mowab,

an hallaka ta da dare!

An lalatar da Kir a Mowab,

an hallaka ta da dare!

2 Dibon ya haura zuwa haikalinta,

zuwa masujadan kan tudu don tă yi kuka;

Mowab ta yi ihu a kan Nebo da Medeba.

An aske kowane kai

an kuma yanke kowane gemu.

3 A tituna sun sa tsummoki a jikunansu;

a kan rufin ɗakuna da kuma dandalin taruwa

dukansu sai makoki suke yi,

sun kwanta suna kuka.

4 Heshbon da Eleyale sun yi kuka da ƙarfi,

aka ji muryoyinsu ko’ina har zuwa Yahaz.

Saboda haka mayaƙan Mowab suka yi kuka da ƙarfi,

har zuciyarsu ta karai.

5 Zuciyata ta yi kuka a kan Mowab;

mutanenta sun gudu har zuwa Zowar,

har zuwa Eglat Shelishiya.

Sun haura zuwa Luhit,

suna tafe suna kuka;

a kan hanyar zuwa Horonayim

suna makoki saboda hallakawarsu.

6 Ruwayen Nimrim sun ƙafe

ciyayin kuma sun bushe;

tsire-tsire duk sun ɓace

babu sauran ɗanyen abu.

7 Saboda haka dukiyar da suka tara suka kuma ajiye

sun ɗauka suka ƙetare Rafin Arabim da su.

8 Ƙugin kukansu ya kai ko’ina a iyakar Mowab;

kururuwarsu ta kai har zuwa Eglayim,

makokinsu ya kai har zuwa Beyer-Elim.

9 Ruwayen Dimon sun cika da jini,

amma zan yi ƙari a kan Dimon,

zan kawo zaki a kan masu gudu na Mowab

da kuma a kan waɗanda suka ragu a ƙasar.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-