Publicidade

Isaías 56

Ceto domin waɗansu

1 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

"Ku riƙe gaskiya

ku yi abin da yake daidai,

gama cetona yana kusa

za a kuma bayyana adalcina nan da nan.

2 Mai albarka ne mutumin da ya aikata wannan,

mutumin da ya riƙe kam

yana kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba,

yana kuma kiyaye kansa daga yin mugun abu."

3 Kada baƙon da ya miƙa kansa ga Ubangiji ya ce,

"Ai Ubangiji zai ware ni daga mutanensa."

Kada kuma wani bābā ya yi gunaguni cewa,

"Ni busasshen itace ne kawai."

4 Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa,

"Wa bābānnin da suna kiyaye Asabbatai,

waɗanda suka zaɓi yin abin da ya gamshe ni

suna kuma riƙe da alkawarina kankan,

5 a gare su cikin haikalina da kuma bangayensa

zan ba da matuni da kuma suna

mafi kyau fiye da ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata;

zan ba su madawwamin sunan

da ba za a raba su da shi ba.

6 Baƙin da suka miƙa kansu ga Ubangiji

don su bauta masa,

su kuma ƙaunaci sunan Ubangiji,

waɗanda kuma suke yin masa sujada,

duk waɗanda suka kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba

suka kuma riƙe alkawarina kankan,

7 waɗannan ne zan kai tsattsarkan dutsena

in sa su yi farin ciki a gidana na addu’a.

Hadayunsu na ƙonawa da sadakokinsu

za su zama abin karɓa a bagadena;

gama za a ce da gidana

gidan addu’a domin dukan al’ummai."

8 Ubangiji Mai Iko Duka ya furta cewa,

zai tattara korarru na Isra’ila,

"Zan ƙara tattaro waɗansu

bayan waɗanda na riga na tattara."

Zargin da Allah ya yi a kan mugaye

9 Ku zo, dukanku namun jeji,

ku zo ku ci, dukanku namun jeji!

10 Matsaran Isra’ila makafi ne,

dukansu jahilai ne;

dukansu bebayen karnuka ne

ba za su iya haushi ba;

suna kwance ne kawai suna mafarki,

suna son barci ba dama.

11 Su karnuka ne masu kwaɗayi;

ba su taɓa ƙoshi.

Su makiyaya ne marasa ganewa;

duk sun nufi inda suka ga dama,

kowa yana nemar wa kansa riba.

12 Kowanne yakan ce, "Zo, bari in samo ruwan inabi!

Bari mu cika cikinmu da barasa!

Gobe ma zai zama kamar yau,

ko ma fiye da haka."

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_12-43-22-