Publicidade

Isaías 21

Annabci a kan Babilon

1 Abin da Allah ya faɗa game da Hamada da take kusa da Teku.

Kamar guguwa mai share cikin ƙasar kudu,

mai hari ya zo daga hamada,

daga ƙasar mai banrazana.

2 An nuna mini mugun wahayi,

mai bashewa ya bashe, mai washewa ya washe.

Elam, ki yi yaƙi! Mediya, ki yi kwanto!

Zan kawo ƙarshen dukan nishe-nishen da ta jawo.

3 Game da wannan jikina yana ciwo,

zafi ya kama ni, kamar na mace mai naƙuda;

na razana game da abin da na ji,

na yi mamakin abin da na gani.

4 Gabana tana ta fāɗuwa,

tsoro ya sa ina rawan jiki;

hasken da nake marmari

ya zo da razana gare ni.

5 Sun shirya teburori,

sun shimfiɗa dardumai,

sun ci, sun sha!

Tashi, ku hafsoshi,

sa mai a garkuwoyi!

6 Ga abin da mai girma ya ce mini,

"Tafi, ka sa mai tsaro

ka kuma sa ya ba da rahoton abin da ya gani.

7 Sa’ad da ya ga kekunan yaƙi

tare da ƙungiyoyin dawakai,

mahaya a kan jakuna,

ko mahaya a kan raƙuma,

to, fa ya zauna a faɗake,

ya kintsa sosai."

8 Mai tsaron kuma ya yi ihu,

"Kowace rana, ranka yă daɗe, nakan tsaya a hasumiyar tsaro;

kowane dare nakan tsaya a wurin aikina.

9 Duba, ga wani mutum tafe a keken yaƙin

tare da ƙungiyar dawakai.

Ya kuma mayar da amsa,

‘Babilon ta fāɗi, ta fāɗi!

Dukan siffofin allolinta

kwance a ragargaje a ƙasa!’ "

10 Ya mutanena, an ragargaje ku a masussuka,

na faɗa muku abin da na ji

daga Ubangiji Maɗaukaki,

daga Allah na Isra’ila.

Annabci a kan Edom

11 Abin da Allah ya faɗa game da Duma,

Wani ya kira ni daga Seyir,

"Mai tsaro, me ya rage a daren?

Mai tsaro, me ya rage a daren?"

12 Mai tsaro ya amsa,

"Safiya ta gabato, haka kuma dare.

In za ka yi tambaya, to, yi tambaya;

sai ka sāke zuwa, ka tambaya."

Annabci a kan Arabiya

13 Abin da Allah ya faɗa game da Arabiya.

Ku ayarin Dedanawa,

ku da kuka sauka a jejin Arabiya,

14 ku kawo ruwa don ƙishirwa;

ku da kuke zama a Tema,

ku kawo abinci don masu gudun hijira.

15 Sun gudu daga takobi,

daga takobin da aka janye,

daga bakan da aka tanƙware

da kuma daga zafin yaƙi.

16 Ga abin da mai girma ya ce mini, "Cikin shekara ɗaya, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, dukan sojojin Kedar za su zo ga ƙarshe. 17 Waɗanda suka yi rai na maharba, jarumawan Kedar, za su zama kaɗan." Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_09-43-29-