Publicidade

Isaías 12

Waƙoƙin yabo

1 A wannan rana za ku ce,

"Zan yabe ka, ya Ubangiji.

Ko da yake a dā ka yi fushi da ni,

amma yanzu ka daina fushi da ni

ka kuwa ta’azantar da ni.

2 Tabbatacce Allah shi ne mai cetona;

zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba.

Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata;

ya zama mai cetona."

3 Da farin ciki zan ɗebo ruwa

daga rijiyoyin ceto.

4 A wannan rana za ku ce,

"Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;

a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai,

a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.

5 Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa;

bari a sanar da wannan ga dukan duniya.

6 Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona,

gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku."

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_06-35-37-