Pular para o conteúdo
Publicidade

Ishaya 32

Mulkin adalci

1 Duba, sarki zai yi mulki cikin adalci

masu mulki kuma su yi mulki da adalci.

2 Kowane mutum zai zama kamar wurin fakewa daga iska

mafaka kuma daga hadari,

kamar rafuffukan ruwa a hamada

da kuma inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa.

3 Sa’an nan idanun waɗanda suka gani ba za su ƙara rufewa ba,

kunnuwan waɗanda suka ji kuma za su saurara.

4 Zuciya marasa haƙuri za su sani su kuma fahimta,

harshen masu ana’ana kuma zai sāke su yi magana sosai.

5 Ba za a ƙara ce da wawa mai girma ba

ko kuwa a ɗaukaka mazambaci.

6 Gama wawa maganar wauta yakan yi,

zuciyarsa ta cika da mugunta,

yana aikata abubuwan rashin sanin Allah

yana baza kurakurai game da Ubangiji;

yana barin mayunwata da yunwa

ya kuma hana masu ƙishirwa ruwan sha.

7 Matakan mazambaci mugaye ne,

yana ƙulla mugayen shirye-shirye

don hallaka talakawa da ƙarairayi,

ko sa’ad da roƙon mai bukata da gaskiya ne.

8 Amma mutumin kirki kan yi shirye-shirye masu kirki,

kuma yakan tsaya a kan ayyukan kirki.

Matan Urushalima

9 Ku matan da kuke zaman jin daɗi,

ku tashi ku saurare ni;

ku yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya,

ku ji abin da zan faɗa!

10 Cikin ɗan lokaci ƙasa da shekara guda

ku da kuke tsammani kuna da kāriya za ku yi rawar jiki;

girbin ya’yan inabi zai kāsa,

girbin ya’yan itatuwa kuma ba zai zo ba.

11 Ku yi rawar jiki, ku mata masu jin daɗi,

ku sha wahala, ku yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya!

Ku tuɓe rigunanku,

ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.

12 Ku bugi ƙirjinku don gonaki masu kyau

don ya’yan inabi

13 da kuma don ƙasar mutanena,

da ƙasar da ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suka yi girma,

I, ku yi kuka saboda dukan gidajen da ake biki

da kuma domin wannan birnin da ake murna a ciki.

14 Za a ƙyale kagarar,

a gudu a bar birnin da ake hayaniya;

mafaka da hasumiyar tsaro za su zama kango har abada,

jin daɗin jakuna, makiyaya don garkuna,

15 sai an zubo Ruhu a kanmu daga sama,

hamada kuma ta zama ƙasar mai taƙi,

gona mai taƙi kuma ta zama kamar kurmi.

16 Aikin gaskiya zai zauna a hamada

adalci kuma zai zauna a ƙasa mai taƙi.

17 Aikin adalci zai zama salama;

tasirin adalci zai zama natsuwa da tabbaci har abada.

18 Mutanena za su zauna lafiya a wuraren salama,

a gidaje masu kāriya,

a wuraren hutun da babu fitina.

19 Ko da yake ƙanƙara za fāɗo a jeji,

a kuma rurrushe birni gaba ɗaya,

20 zai zama muku da albarka,

ku da kuke shuki iri kusa da kowane rafi,

kuna kuma barin lafiyayyiyar makiyaya domin shanu da jakunanku.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também