Publicidade

Isaías 31

Kaiton waɗanda suke dogara ga Masar

1 Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako,

waɗanda suke dogara ga dawakai,

waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu

da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu,

amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila,

ko ya nemi taimako daga Ubangiji.

2 Shi ma yana da hikima kuma zai iya kawo masifa;

ba ya janye kalmominsa.

Zai yi gāba da gidan mugu,

gāba da waɗanda suke taimakon masu aikata mugunta.

3 Amma Masarawa mutane ne ba Allah ba;

dawakansu nama da jini ne ba ruhu ba.

Sa’ad da Ubangiji ya miƙa hannunsa,

shi da yake taimako zai yi tuntuɓe

shi da aka taimaka zai fāɗi;

dukansu biyu za su hallaka tare.

4 Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini,

"Kamar yadda zaki kan yi ruri

babban zaki a kan abin da ya yi farauta,

kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyaya

sun taru wuri ɗaya a kansa,

ba zai jijjigu ta wurin ihunsu ba

ko ya damu da kiraye-kirayensu,

ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai sauko

don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa.

5 Kamar tsuntsaye masu shawagi a sama

haka Ubangiji Maɗaukaki zai kiyaye Urushalima;

zai kāre ta ya kuma fanshe ta,

zai ‘ƙetare’ ta ya kuma kuɓutar da ita."

6 Ku dawo gare shi ku da kuka yi masa babban tayarwa, ya Isra’ilawa. 7 Gama a wannan rana kowannenku zai ƙi gumakan azurfa da zinariya da hannuwanku masu zunubi suka yi.

8 "Za a karkashe Assuriyawa da takobin da ba na yin mutum ba;

takobi, da ba na yin mutum ba, zai cinye.

Za su gudu daga takobi

za a kuma sa samarinsu aikin dole.

9 Kagararsu za tă fāɗi saboda razana;

da ganin matsayin yaƙin, shugabannin yaƙinsu za su firgita,"

in ji Ubangiji,

wanda wutarsa tana a Sihiyona,

wanda matoyarsa tana a Urushalima.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-