Pular para o conteúdo
Publicidade

Ishaya 2

Dutsen Ubangiji

1 Ga abin da Ishaya ɗan Amoz ya gani game da Yahuda da Urushalima.

2 A kwanaki masu zuwa

za a kafa dutsen haikalin Ubangiji

a matsayin babba cikin duwatsu;

za a daga shi bisa tuddai,

kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi.

3 Mutane da yawa za su zo su ce,

"Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji,

zuwa gidan Allah na Yaƙub.

Zai koya mana hanyoyinsa,

domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa."

Dokar za fito daga Sihiyona,

maganar Ubangiji daga Urushalima.

4 Zai shari’anta tsakanin al’ummai

zai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa.

Za su mai da takubansu su zama garemani

māsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa.

Al’umma ba za ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba,

ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi.

5 Ki zo, ya gidan Yaƙub,

bari mu yi tafiya a hasken Ubangiji.

Ranar Ubangiji

6 Ka rabu da mutanenka,

gidan Yaƙub.

Sun cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas;

suna yin duba kamar Filistiyawa

suna tafa hannuwa tare da marasa sanin Allah.

7 Ƙasarsu ta cika da azurfa da zinariya;

dukiyarsu kuma ba iyaka.

Ƙasarsu ta cika da dawakai;

kekunan yaƙinsu kuma ba iyaka.

8 Ƙasarsu ta cika da gumaka;

sukan rusuna ga aikin hannuwansu,

ga abin da yatsotsinsu suka yi.

9 Saboda an jawo mutum ƙasa

aka kuma ƙasƙantar da ɗan adam,

kada ku gafarta musu.2.9 Ko kuwa kada a ɗaga su

10 Ku tafi cikin duwatsu,

ku ɓuya cikin ƙasa

daga razanar Ubangiji

da kuma darajar ɗaukakarsa!

11 Za a ƙasƙantar da mai girman kai

za a kuma lalatar da fariyar masu ɗaga kai;

Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana.

12 Ubangiji Maɗaukaki yana da rana ajiye

domin dukan masu girman kai da masu fariya

domin dukan waɗanda aka ɗaukaka

(zai kuwa ƙasƙantar da su),

13 domin dukan al’ul na Lebanon, masu tsayi da masu fariya,

da kuma dukan itatuwan oak na Bashan,

14 domin dukan dogayen duwatsu

da kuma tuddai masu tsayi,

15 domin kowace doguwar hasumiya

da kowace katanga mai ƙarfi,

16 domin kowane jirgin ruwan kasuwanci2.16 Da Ibraniyanci kowane jirgin ruwan Tarshish

da kuma jirgi mafi girma mafi kyau.

17 Za a jawo mai girman kai ƙasa

a kuma ƙasƙantar da mai ɗaga kai;

Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana,

18 za a kuma kawar da gumaka ƙaƙaf.

19 Mutane za su gudu zuwa kogwannin duwatsu

da kuma ramummuka a ƙasa

daga razanar Ubangiji

da kuma darajar ɗaukakarsa,

sa’ad da ya tashi don girgiza duniya.

20 A wannan rana mutane za su zubar wa

jaba da jamage

gumakansu na azurfa da gumakansu na zinariya

da suka yi don su bauta musu.

21 Za su gudu zuwa kogwannin duwatsu

da kuma zuwa tsagaggun duwatsu

daga razanar Ubangiji

da kuma darajar ɗaukakarsa,

sa’ad da ya tashi don girgiza duniya.

22 Ku daina dogara ga mutum,

wanda numfashi ne kawai yake da shi a hancinsa.

Wace daraja gare shi?

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também