Publicidade

Jó 25

Bildad

1 Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,

2 "Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa;

yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama.

3 Za a iya ƙirga rundunarsa?

A kan wane ne ba ya haska haskensa?

4 Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?

Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki?

5 In har wata da taurari

ba su da tsarki a idanunsa,

6 mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai.

Me mutum ya daɗa a gaban Allah!"

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-