Pular para o conteúdo
Publicidade

Ayuba 16

Ayuba

1 Sai Ayuba ya amsa,

2 "Na ji abubuwa da yawa kamar waɗannan;

dukanku ba ku iya ta’aziyya ba!

3 Dogayen surutanku ba sa ƙare ne?

Me yake sa kuke ta yin waɗannan surutai har kuke cin gaba da yin gardama?

4 Ni ma zan iya yin maganganu kamar yadda kuke yi

in da kuna cikin halin da nake;

zan iya faɗar duk abubuwan da kuke faɗi,

in kaɗa muku kaina.

5 Amma bakina zai ƙarfafa ku;

ta’aziyyar da za fito daga bakina za kawar muku da ɓacin zuciyarku.

6 "Duk da haka in na yi magana, ba na samun sauƙi;

in ma na yi shiru zafin ba ya tafiya.

7 Ba shakka ya Allah ka gajiyar da ni;

ka ɓata gidana gaba ɗaya.

8 Ka daure ni, ya kuma zama shaida;

yadda na rame sai ƙasusuwa, wannan ya sa ake gani kamar don ni mai zunubi ne shi ya sa.

9 Allah ya kai mini hari ya yi kaca-kaca da ni cikin fushinsa

yana cizon haƙoransa don fushin da yake yi da ni;

ya zura mini ido.

10 Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni;

suka yi mini ba’a

suka haɗu suka tayar mini.

11 Allah ya bashe ni ga mugayen mutane,

ya jefa ni hannun mugaye.

12 ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai;

amma ya ragargaza ni; ya shaƙe ni a wuya;

ya murƙushe ni na zama abin barata gare shi;

13 maharbansa sun kewaye ni.

Ba tausayi, ya soke ni a ƙodata

har jini ya zuba a ƙasa.

14 Ya ji mini rauni a kai a kai

ya auko mini kamar mai yaƙi.

15 "Ina makoki saye da tsummoki

na ɓoye fuskata a cikin ƙura.

16 Fuskata ta yi ja don kuka

idanuna sun kukumbura;

17 duk da haka hannuwana ba su aikata ɓarna ba

kuma addu’ata mai tsabta ce.

18 "Ya duniya, kada ki ɓoye jinina;

bari yi kuka a madadina!

19 Ko yanzu haka shaidata tana sama;

wanda zai tsaya mini yana sama.

20 Shi mai yin roƙo a madadina abokina ne

yayinda nake kuka ga Allah;

21 a madadin mutum ya yi roƙo ga Allah

kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.

22 "Shekaru kaɗan suka rage

in kama hanyar da ba a komawa.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também