Pular para o conteúdo
Publicidade

Ayuba 15

Elifaz

1 Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,

2 "Mutum mai hikima zai amsa da surutai marasa kan gado

ko cika cikinsa da iskar gabas?

3 Ko zai yi gardama da maganganun wofi

maganganu marasa amfani?

4 Amma ka ma rena Allah

ka hana a yi addu’a gare shi.

5 Zunubanka ne suke gaya maka abin da za ka ce;

kana magana kamar mai wayo.

6 Bakinka zai kai ka baro, ba nawa ba;

maganar bakinka za juya a kanka.

7 "Kai ne mutum na farko da aka fara haihuwa?

Ko kai ne aka fara halitta kafin tuddai?

8 Kana sauraron shawarar Allah?

Ko kana gani kai kaɗai ne mai hikima?

9 Me ka sani da ba mu sani ba?

Wane fahimi kake da shi da ba mu da shi?

10 Masu furfura da tsofaffi suna gefenmu

mutanen da sun girme babanka.

11 Ta’aziyyar Allah ba ishe ka ba.

Maganarsa mai laushi ba ishe ka ba?

12 Don me ka bar zuciyarka ta kwashe ka,

kuma don me idanunka suke haske,

13 har kake fushi da Allah

kake kuma faɗar waɗannan maganganu daga bakinka?

14 "Mene ne mutum, har da zai zama da tsarki,

ko kuma mace ta haife shi, har iya zama mai adalci?

15 In Allah bai nuna amincewa ga tsarkakansa ba,

in har sammai ba su da tsarki a idonsa,

16 mutum fa, wanda yake da mugunta da lalacewa,

wanda yake shan mugunta kamar ruwa!

17 "Ka saurare ni, zan kuma yi maka bayani;

bari in gaya maka abin da na gani,

18 abin da masu hikima suka ce,

ba tare da sun ɓoye wani abu da suka samu daga wurin iyayensu ba

19 (waɗanda su ne masu ƙasar

kafin baƙi su shigo ƙasar).

20 Dukan kwanakin ransa mugu yana shan wahala,

wahala kaɗai zai yi ta sha.

21 Ƙara mai bantsoro za cika kunnuwansa

yan fashi za su kai masa hari.

22 Yana jin tsoron duhu

domin za a kashe shi da takobi.

23 Yana ta yawo, abinci don ungulaye;15.23 Ko kuwa yawo, neman abinci

ya san ranar duhu tana kusa.

24 Ɓacin rai da baƙin ciki sun cika shi,

kamar sarkin da yake shirin yaƙi,

25 domin ya nuna wa Allah yatsa

ya rena Allah Maɗaukaki,

26 ya tasar masa da faɗa

da garkuwa mai kauri da kuma ƙarfi.

27 "Ko da yake fuskarsa ta cika da kumatu

kuma yana da tsoka ko’ina,

28 zai yi gādon garuruwan da suka lalace,

da kuma gidajen da ba wanda yake zama a ciki,

gidajen da sun zama tarkace.

29 Ba zai sāke zama mai arziki ba, dukiyarsa ba za dawwama ba,

abin da ya mallaka kuma ba zai bazu a ƙasar ba.

30 Ba zai tsere wa duhu ba;

wuta za ƙona rassansa,

kuma numfashi daga bakin Allah zai hallaka shi.

31 Kada ruɗi kansa ta wurin dogara ga abin da ba shi da amfani

domin ba zai samu wani abu ba daga ciki.

32 Kafin lokacinsa cika, za a gama biyansa duka,

kuma rassansa ba za su ba da amfani ba.

33 Zai zama kamar itacen inabi wanda ya’yansa suka kakkaɓe kafin su nuna,

kamar itacen zaitun zai zubar da furensa.

34 Gama marasa tsoron Allah za su zama marasa ba da ya’ya,

wuta kuma za ƙona tenti na masu son cin hanci.

35 Suna yin cikin rikici su kuma haifi mugunta;

cikinsu yana cike da ruɗami."

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também