Ano novo
O Ano Novo é oportunidade de renovação e consagração. A Bíblia convida a esquecer o que ficou para trás e avançar em fé, confiança e esperança em Deus.
’Yan’uwa, ban ɗauki kaina a kan cewa na riga na sami abin ba. Sai dai abu guda nake yi. Ina mantawa da abin da yake baya, ina kuma nacewa zuwa ga samun abin da yake gaba, ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu.
Ba cewa na riga na sami dukan wannan ba ne, ko kuma an riga an mai da ni cikakke ba, sai dai ina nacewa don in kai ga samun abin da Kiristi Yesu ya riƙe ni saboda shi. ’Yan’uwa, ban ɗauki kaina a kan cewa na riga na sami abin ba. Sai dai abu guda nake yi. Ina mantawa da abin da yake baya, ina kuma nacewa zuwa ga samun abin da yake gaba, ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu.
Nacewa zuwa ga manufar
Dukanmu da muka balaga ya kamata mu yi wannan irin ganin abubuwa. In kuwa saboda wani dalili tunaninku ya yi dabam, Allah zai bayyana muku wannan ma.
Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!
Yabo ga Allah domin bege mai rai
Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu,
Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah,
ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina.
Kada ka fid da ni daga gabanka
ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni.
Ka natsu a gaban Ubangiji
ka kuma jira da haƙuri gare shi;
kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu,
sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.
Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau;
mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.
amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.
Zan yayyafa muku ruwa mai tsabta, zan kuwa tsarkake ku daga dukan ƙazantarku daga kuma dukan gumakanku. Zan ba ku sabuwa zuciya in kuma sa sabon ruhu a cikinku; zan fid da zuciyar dutse in kuma ba ku zuciyar nama. Zan kuma sa Ruhuna a cikinku in kuma motsa ku ku bi ƙa’idodina ku kuma kiyaye dokokina.
Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.
Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.
Ya yi kowane abu da kyau a lokacinsa. Ya kuma sa matuƙa a zukatan mutane, duk da haka sun kāsa gane abin da Allah ya yi daga farko zuwa ƙarshe.
Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa. Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.
Yin fahariya game da gobe
Yanzu fa sai ku saurara, ku da kuke cewa, "Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni, mu yi shekara a can, mu yi kasuwanci, mu ci riba." Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan yă ɓace. A maimakon haka, ya kamata ku ce, "In Ubangiji ya yarda, muna kuma a raye, za mu yi wannan ko wancan." Ga shi, kuna fariya da taƙama. Duk irin wannan taƙama mugun abu ne. Saboda haka, duk wanda ya san abu mai kyan da ya kamata yă yi, bai kuwa yi ba, ya yi zunubi ke nan.