Publicidade

Arca da aliança

Por Bíblia Online

A Arca da Aliança era o símbolo mais sagrado de Israel — representava a presença de Deus no meio do seu povo. Sobre ela brilhava a glória do Senhor entre os querubins.

Akwatin alkawari

"Ka sa a yi akwatin alkawarin da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi. Ka dalaye shi da zinariya zalla ciki da waje, za ka yi wa gefe-gefensa ado da gurun zinariya. Ka kewaye akwatin da zoban zinariya huɗu ka kuma haɗa su da ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a kowane gefe. Sa’an nan ka yi sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya. Ka sa sandunan a cikin zoban, a gefen akwatin domin ɗaukansa. Sanduna za su kasance a cikin waɗannan zoban akwatin alkawarin; ba za a cire su ba. Sa’an nan ka sa Shaidar da zan ba ka, a cikin akwatin.

"Ka yi murfin kafara da zinariya zalla, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi. Ka kuma yi kerubobi biyu da zinariyar da aka ƙera, ka sa a gefen nan biyu na murfin. Ka yi kerubobi biyu, ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a ɗayan gefen; za ka manne su a kan murfin, su zama abu ɗaya. Kerubobin su kasance da fikafikansu a buɗe, domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin. Ka sa murfin a bisa akwatin ka kuma sa allunan dokokin alkawarin da zan ba ka a ciki.

Can, a bisa murfin da yake tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari na Shaida, zan sadu da kai, in kuma ba ka dukan umarnai domin Isra’ilawa.

Akwatin alkawari

Bezalel ya yi akwatin alkawari da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kamu ɗaya da rabi.

Kafawa tabanakul

Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, "Ka kafa tabanakul, da Tentin Sujada, a kan rana ta fari ga watan fari. Ka sa akwatin Alkawari a cikinsa, sa’an nan ka rufe shi da labule.

Ya ɗauki dokokin Alkawari ya sa a cikin akwatin, ya kuma zura sandunan a zoban akwatin, sa’an nan ya sa murfin kafara a bisansa. Sai ya kawo akwatin a cikin tabanakul, ya kuma rataye labulen rufewa ya tsare akwatin Alkawarin, yadda Ubangiji ya umarce shi.

Sa’ad da Musa ya shiga Tentin Sujada don yi magana da Ubangiji, sai ya ji murya tana magana da shi daga tsakanin kerubobi biyu a bisa murfin akwatin Alkawari. A ta haka Ubangiji ya yi masa magana.

Saboda haka suka kama hanya daga dutsen Ubangiji, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji ya ja gabansu a waɗannan kwanaki uku, don samo musu masauƙi. A duk lokacin da suka tashi daga sansani, girgijen Ubangiji ya inuwantar da su da rana.

Duk kuma sa’ad da akwatin ya kama hanya, sai Musa ya ce,

"Ka tashi, ya Ubangiji!

Ka sa maƙiyanka su warwatse;

masu ƙinka kuma su gudu a gabanka."

Duk sa’ad da akwatin ya sauka kuma, sai Musa ya ce,

"Ka komo, ya Ubangiji,

a wurin dubban da ba a iya ƙidayawa na iyalan Isra’ila."

Tohuwar sandar Haruna

Ubangiji ya ce wa Musa, "Ka yi magana da Isra’ilawa, ka kuma karɓi sanduna goma sha biyu daga wurinsu, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu. Ka rubuta sunan kowa a sandansa. A kan sandan Lawi kuwa ka rubuta sunan Haruna, gama dole a sami sanda ɗaya saboda shugaban gidan kakanninsu. Ka ajiye su a Tentin Sujada, a gaba akwatin Alkawari, inda zan sadu da kai. Sandan mutumin da na zaɓa zai yi toho, da haka zan raba kaina da gunagunin da Isra’ilawa suke yi."

Saboda haka Musa ya yi magana da Isra’ilawa, sai shugabanninsu suka ba shi sanduna goma sha biyu, sanda ɗaya don shugaba, bisa ga gidajen kakanninsu, sandan Haruna kuma yana a cikinsu. Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada.

Kashegari da Musa ya shiga cikin Tentin Sujada sai ga sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi ya’yan almon. Sai Musa ya fitar wa dukan Isra’ilawa dukan sandunan da suke daga gaban Ubangiji. Suka duba, kowa kuma ya ɗauki sandansa.

Ubangiji ya ce wa Musa, "Ka mayar da sandan Haruna a akwatin Alkawari, don a ajiye shi alama ga masu tawaye. Wannan zai kawo ƙarshen gunaguninsu a kaina, domin kada su mutu." Musa kuwa ya aikata kamar dai yadda Ubangiji ya umarce shi.

Saboda haka sa’ad da mutanen suka tashi don su ƙetare Urdun, firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin suka sha gaba. Da kaka Urdun yakan cika makil da ruwa. Duk da haka da zarar firistoci masu ɗauke da akwatin alkawari suka tsoma ƙafafunsu a gefen ruwa, sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru a wuri ɗaya ya yi tudu daga nan har zuwa wani garin da ake kira Adam kusa da Zaretan, ruwan da yake gangarowa zuwa Tekun Araba (Tekun Gishiri) kuma ya yanke gaba ɗaya. Sai mutane suka ƙetare kusa da Yeriko. Firistocin kuwa da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya daram a kan busasshiyar ƙasa a tsakiyar Urdun a lokacin da Isra’ilawa suka ƙetarewa, har sai da dukan mutane suka gama ƙetarewa.

Firistocin kuwa suka fito daga kogin ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji. Nan da nan da ƙafafunsu suka taɓa busasshiyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya gangaro ya cika kogin kamar yadda yake a .

Ƙofofin Yeriko kuwa a kulle suke ciki da waje saboda Isra’ilawa, ba mai fita babu kuma mai shiga.

Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, "Duba, na ba ka nasara a kan Yeriko, duk da sarkinta da mayaƙanta. Da kai da dukan sojoji, ku zaga birnin sau ɗaya kullum. Ku yi haka har kwana shida. Ka sa firistoci guda bakwai su riƙe ƙahoni raguna su kasance a gaban akwatin alkawari. A rana ta bakwai sai ku zaga birnin sau bakwai, firistocin suna busa ƙahoni. Sa’ad da kuka ji sun ɗauki dogon lokaci suna busa ƙaho, sai mutane gaba ɗaya su da murya su yi ihu da ƙarfi; katangar birnin kuwa za rushe, sai sojoji su haura, ko wanne nufi inda ya fuskanta kai tsaye."

Yoshuwa ɗan Nun kuwa ya kira firistoci ya ce musu, "Ku ɗauki akwatin alkawari, ku sa firistoci guda bakwai su riƙe ƙahoni su kasance a gabansa." Sai ya umarci jama’a ya ce, "Mu je zuwa! Ku zaga birnin, masu tsaro da makamai su shiga gaban akwatin alkawarin Ubangiji."

Da aka busa ƙahoni, sojoji suka yi ihu, da jin ƙarar ƙahoni, mutane suka kuma yi ihu, sai katangar ta rushe; dukan mutanen kuwa suka shiga birnin kai tsaye, suka yi nasara a kanta.

Filistiyawa suka tunƙuro mayaƙansu domin su sadu da Isra’ilawa, yaƙi kuwa ya yi tsanani har Isra’ilawa suka sha kashi a hannun Filistiyawa. Filistiyawa suka kashe Isra’ilawa kusan mutum dubu huɗu a bakin dāgā. Lokacin da mayaƙan suka komo sansani, dattawan Isra’ilawa suka yi tambaya suka ce, "Me ya sa Ubangiji ya sa muka sha ɗibga a hannun Filistiyawa? Bari mu kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Shilo. Domin tafi tare da mu ba mu nasara kan abokan gābanmu."

Saboda haka mutanen suka aika waɗansu maza zuwa Shilo, suka kuwa tafi suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Maɗaukaki wanda yake zaune tsakanin Kerubobi. Ya’yan Eli biyun nan Hofni da Finehas suna wurin tare da akwatin alkawarin Ubangiji.

Da aka shigo da akwatin alkawarin Ubangiji a cikin sansani, sai Isra’ilawa suka da babbar murya har ƙasa ta jijjiga. Da jin wannan, Filistiyawa suka yi tambaya suka ce, "Me ke kawo wannan ihu mai ƙarfi haka a sansanin Isra’ilawa?"

Da suka gane cewa akwatin alkawarin Ubangiji ne ya shiga sansanin, sai Filistiyawa suka ji tsoro, suka ce, "Wani allah ya shiga cikin sansanin. Mun shiga uku! Ba a taɓa yin wani abu haka ba. Kaiton mu! Wa zai kuɓutar da mu daga hannun waɗannan manyan alloli? Su ne allolin da suka buga Masarawa da irin annoba masu yawa a jeji. Ku yi ƙarfin hali, ku yi mazantaka, ku Filistiyawa, domin kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suke a gare ku. Ku yi mazantaka, ku yi yaƙi."

Saboda haka Filistiyawa suka yi yaƙi, Isra’ilawa kuwa suka sha ɗibga, kowane mutum kuwa ya gudu zuwa tentinsa. Kisan kuwa ya yi muni ƙwarai. Isra’ilawa sun rasa mayaƙa dubu talatin. Aka ƙwace akwatin alkawarin Ubangiji. Aka kuma kashe ya’yan Eli biyu, Hofni da Finehas.

Hannun Ubangiji kuwa ya yi nauyi a bisa Ashdod da kewayenta. Ya kawo hallaka ga dukansu, ya kuma buga su da marurai. Da mutanen Ashdod suka ga abin da yake faruwa, sai suka ce, "Lalle Akwatin Alkawarin Allah na Isra’ila ba zai kasance da mu ba, domin hannunsa yana da nauyi a kanmu da bisan Dagon allahnmu." Saboda haka suka kira duka shugabannin Filistiyawa suka tambaye su, suka ce, "Me za mu da akwatin alkawarin Allahn Isra’ila?"

Sai suka amsa suka ce, "A ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila a kai shi Gat." Sai suka ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila.

Amma bayan sun kai shi can, sai hannun Ubangiji ya yi gāba da birnin, aka jefa shi cikin wani mawuyacin hali. Ya buga mutanen birnin da marurai, babba da yaro. Sai suka aika da akwatin alkawarin Allah zuwa Ekron.

Yayinda akwatin alkawarin Allah yana shiga cikin Ekron, mutanen Ekron suka yi ihu, suka ce, "An kawo mana akwatin alkawarin Allah na Isra’ila domin kashe mu da mutanenmu." Saboda haka suka kira ga dukan shugabannin Filistiyawa suka ce, "Ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila inda ya fito; in ba haka ba zai kashe mu da mutanenmu." Gama mutuwa ta cika garin da tsoro. Hannun Allah ya yi nauyi a kansa.

An komar da akwatin alkawari a Isra’ila

Lokacin da akwatin alkawarin Ubangiji ya kai wata bakwai a ƙasar Filistiyawa. Filistiyawa suka kira firistoci da bokaye suka ce, "Me za mu yi da akwatin alkawarin Ubangiji? Ku gaya mana yadda za mu komar da shi inda ya fito."

Suka ce, in za ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila kada ku komar da shi hannu wofi; amma ku tabbata kun aika da hadaya don laifi zuwa wurinsa. Sa’an nan za ku warke ku kuma san dalilin da ya sa bai cire hannunsa a kanku ba.

Suka yi haka. Suka ɗauki shanun tatsa guda biyu suka ɗaura musu keken shanu, suka tsare yan maruƙansu a gida. Suka aza akwatin alkawarin Ubangiji a bisa keken shanun tare da akwatin siffofin ɓerayen zinariya da siffofin maruran. Sai shanun suka miƙe zuwa Bet-Shemesh. Suka bi hanya daidai, ba su juya dama ko hagu ba. Shugabannin Filistiyawa suka bi har zuwa iyakar ƙasar Bet-Shemesh.

A lokacin kuwa mutanen Bet-Shemesh suna girbin alkamansu a kwari da suka ɗaga ido suka hangi akwatin alkawarin Ubangiji, sai suka yi farin ciki ganinsa. Keken shanun ya zo filin Yoshuwa a Bet-Shemesh ya tsaya a gefen wani babban dutse. Mutanen suka faskare keken shanun suka miƙa shanun hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Lawiyawa suka saukar da akwatin alkawarin Ubangiji tare da babban akwati mai siffofin zinariya na ɓeraye da marurai suka ajiye su a kan ƙaton dutse. A wannan rana mutanen Bet-Shemesh suka miƙa hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu ga Ubangiji.

Mutanen Kiriyat Yeyarim suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji. Suka kai a gidan Abinadab da ke kan tudu, suka keɓe Eleyazar ɗansa lura da akwatin alkawarin Ubangiji. Akwatin Alkawarin ya daɗe a Kiriyat Yeyarim ya kai shekara ashirin cif.

Sama’ila ya ci Filistiyawa da yaƙi a Mizfa

Sai dukan mutanen Isra’ila suka yi makoki suka nemi Ubangiji.

To, sai aka faɗa wa Sarki Dawuda cewa, "Ubangiji ya sa wa gidan Obed-Edom albarka da dukan abin da yake da shi, saboda akwatin alkawarin Allah." Saboda haka sai Dawuda ya gangara ya hauro da akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-Edom zuwa Birnin Dawuda da farin ciki. Sa’ad da waɗanda suke ɗaukan akwatin alkawarin Ubangiji suka yi tafiya taki shida, sai yi hadayar bijimi da saniya mai ƙiba. Dawuda, sanye da efod lilin, ya yi ta rawa a gaban Ubangiji da dukan ƙarfinsa, yayinda shi da dukan gidan Isra’ila suka hauro da akwatin alkawarin Ubangiji da sowa da kuma busar ƙahoni.

An kawo akwatin alkawari a haikali

Sai Sarki Solomon ya tattara dattawan Urushalima a gabansa, da dukan shugabannin kabilu, da shugabannin iyalan Isra’ilawa, domin su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Sihiyona, Birnin Dawuda. Dukan mutanen Isra’ila suka tattaru a gaban Sarki Solomon a lokacin biki, a watan Etanim, wato, wata na bakwai.

Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka iso, sai firistoci suka ɗauki akwatin alkawarin, suka haura da akwatin alkawarin Ubangiji da kuma Tentin Sujada, da dukan kayayyaki masu tsarkin da suke cikinsa. Firistoci da Lawiyawa suka ɗauko su, sai Sarki Solomon da dukan taron Isra’ila da suka tattaru kewaye da shi a gaban akwatin alkawari, suka yi ta miƙa hadayar tumaki da bijimai masu yawa da ba a iya lissaftawa, ko ƙirgawa.

Sa’an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji inda aka shirya masa, can ciki cikin haikali, a Wuri Mafi Tsarki, aka kuma sa shi a ƙarƙashin fikafikan kerubobin. Kerubobin sun buɗe fikafikansu a bisa wurin da akwatin alkawarin yake, suka inuwartar da akwatin alkawarin da sandunan ɗaukansa. Waɗannan sandunan sun yi tsawo har ana iya ganin bakinsu daga Wuri Mai Tsarki a gaban wuri mai tsarki na can ciki, amma ba a iya ganinsu daga waje na Wuri Mai Tsarki ba. Suna nan kuwa a can har wa yau. Ba kome a cikin akwatin alkawarin, sai dai alluna na dutse guda biyu waɗanda Musa ya ajiye a ciki tun a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da Isra’ilawa bayan sun fito Masar.

Sa’ad da firistoci suka janye daga Wuri Mai Tsarki, sai girgije ya cika haikalin Ubangiji. Firistocin kuwa ba su iya yin hidimarsu ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika haikalinsa.

"Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya," in ji Ubangiji, "gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona. Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi. A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar," in ji Ubangiji, "mutane ba za su ƙara yin magana a kan, Akwatin alkawarin Ubangiji ba.Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba.

Sujada a cikin tabanakul na duniya

Alkawarin farko ya ƙunshi ƙa’idodi don sujada da kuma tsattsarkan wuri a duniya. An kafa tabanakul. A cikin ɗakinsa na farko akwai wurin ajiye fitila, tebur da kuma keɓaɓɓen burodi; an kira wannan Wuri Mai Tsarki. Sa’an nan akwai labule, kuma a bayan labulen akwai ɗaki na biyu da ake kira Wuri Mafi Tsarki, wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari. A bisa akwatin alkawarin kuwa akwai kerubobi na Ɗaukaka, waɗanda suka inuwantar da murfin kafara da fikafikansu. Sai dai ba za mu tattauna waɗannan abubuwa dalla-dalla a yanzu ba.

Sa’an nan aka buɗe haikalin Allah da yake a sama, kuma a cikin haikalinsa aka ga akwatin alkawarinsa. Sai kuwa ga walƙiya, ƙararraki, tsawa, girgizar ƙasa, da kuma ƙanƙara masu girma.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-