Pular para o conteúdo
Publicidade

Amos 1

1 Kalmomin Amos, ɗaya daga cikin makiyayan Tekowa, abubuwan da ya gani game da Isra’ila shekaru biyu kafin a yi girgizar ƙasa, a lokacin da Uzziya yake sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yowash kuma yake sarkin Isra’ila.

2 Ya ce,

"Ubangiji ya yi ruri daga Sihiyona

ya kuma yi tsawa daga Urushalima;

wuraren kiwo duk sun bushe,

dutsen Karmel kuma ya yi yaushi."

Hukunci a kan maƙwabtan Isra’ila

3 Ga abin da Ubangiji ya ce,

"Saboda zunubai uku na Damaskus,

har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.

Domin sun ci zalunci Gileyad

zalunci mai tsanani,

4 zan sa wuta a gidan Hazayel,

da za ƙona kagarun Ben-Hadad.

5 Zan kakkarye ƙofofin Bet-Damaskus;

zan hallaka sarkin da yake cikin1.5 Ko kuwa mazaunan Kwarin Awen1.5 Awen yana nufin mugunta.

da kuma mai riƙe da sandar mulkin Bet-Eden.

Mutanen Aram za su je bauta a ƙasar Kir,"

in ji Ubangiji.

6 Ga abin da Ubangiji ya ce,

"Saboda zunubai uku na Gaza,

har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.

Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya

sun sayar wa Edom,

7 Zan aika da wuta a katangar Gaza

ta ƙone duk kagarunta.

8 Zan hallaka sarkin1.8 Ko kuwa mazaunan Ashdod

da kuma mai riƙe da sandar mulki na Ashkelon.

Zan hukunta Ekron,

har sai dukan Filistiyawa sun mutu,"

in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

9 Ga abin da Ubangiji ya ce,

"Saboda zunubai uku na Taya,

har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.

Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun kai su bauta a Edom,

ba su kula da yarjejjeniyar da aka yi ta zama kamar yan’uwa ba,

10 zan aika da wuta a Taya,

da za ƙone kagarunta."

11 Ga abin da Ubangiji ya ce,

"Saboda zunubai uku na Edom,

har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba.

Don ya fafari ɗan’uwansa da takobi,

babu tausayi,

domin ya ci gaba da fusata

bai yarda huce daga fushinsa ba.

12 Zan aika wuta a Teman

da za ƙone kagarun Bozra."

13 Ga abin da Ubangiji ya ce,

"Saboda zunubai uku na Ammon,

har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba.

Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu

don kawai ƙwace ƙasar.

14 Zan sa wuta a katangar Rabba

da za ƙone kagarunta

za a yi kururuwa a ranar yaƙi,

faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri.

15 Sarkinta1.15 Ko kuwa Molek; Ibraniyawa malkam zai je bauta,

shi da ma’aikatansa,"

in ji Ubangiji.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também