Pular para o conteúdo
Publicidade

Amos 6

Kaito ga zaman sakewa

1 Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona,

da ku waɗanda kuke ji zama a Dutsen Samariya lafiya ne,

ku manyan mutanen ƙasar da take sananniya,

waɗanda mutanen Isra’ila suke zuwa!

2 Ku je Kalne ku dube ta;

ku wuce daga can zuwa Hamat-rabba,

sa’an nan ku gangara zuwa Gat a Filistiya.

Sun fi masarautunku biyu ne?

Ƙasarsu ta fi taku girma?

3 Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan muguwar rana

kuna kuma jawo mulkin tashin hankali kusa.

4 Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa

kuna mimmiƙe a kan kujerunku.

Kuna cin naman ƙibabbun raguna

da na ƙosassun yan maruƙa.

5 Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yi

kuna ƙirƙiro waƙoƙi a kan kayan kaɗe-kaɗe.

6 Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi

kuna kuma shafa mai mafi kyau,

amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama.

7 Saboda haka za ku zama na farkon da za su tafi zaman bauta;

bukukkuwanku da shagulgulanku za su ƙare.

Ubangiji yana ƙyamar girmankan Isra’ila

8 Ubangiji Mai Iko Duka da kansa ya rantse, Ubangiji Allah Maɗaukaki ya furta,

"Ina ƙyamar girman kan Yaƙub,

ba na kuma son kagarunsa;

zan ba da birnin

da duk abin da yake cikinta."

9 Ko da mutum goma ne suka ragu a gida guda, su ma za su mutu. 10 In kuma wani dangi ya shiga don fitar da gawawwakin ƙone ya kuwa tambayi wani wanda yake ɓoye a can, yana cewa, "Akwai wani tare da kai?" Ya kuwa ce, "Babu," sai ce, "Kul! Kada mu ambaci sunan Ubangiji."

11 Gama Ubangiji ya ba da umarni,

zai kuma ragargaza babban gidan nan kucu-kucu

ƙaramin gidan kuwa zai yi rugu-rugu da shi.

12 Dawakai sukan yi gudu a kan duwatsu?

Wani yana iya yin noma a teku da shanun noma?

Amma ga shi kun mai da gaskiya ta zama dafi

amfanin adalci kuma ya zama ɗaci,

13 ku da kuke murna saboda an ci Lo Debar6.13 Lo Debar yana nufin wofi. da yaƙi

kuka kuma ce, "Ba da ƙarfinmu ne muka ƙwace Karnayim6.13 Karnayim yana nufin ƙahoni; ƙaho a nan yana a matsayin ƙarfi. ba?"

14 Gama Ubangiji Allah Maɗaukaki ya ce,

"Zan sa wata ƙasa ta tayar muku, ya ku gidan Isra’ila,

wadda za matsa muku tun

daga Lebo6.14 Ko kuwa daga mashigi zuwa Hamat zuwa kwarin Araba."

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também