Publicidade

Arrependimento

Por Bíblia Online

O arrependimento é a porta da graça. A Bíblia declara que Deus não deseja a morte do ímpio, mas que se converta e viva. Arrependei-vos, pois o Reino dos Céus está próximo.

Chamado ao arrependimento

Arrependei-vos, porque o Reino dos Céus está próximo. Quem se arrepende e confessa encontra restauração e perdão.

Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, "Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa."

Ku yi ayyukan da suka dace da tuba.

Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba. Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi."

Yana cewa, "Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!"

Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.

Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba."

Bitrus ya amsa, "Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki.

Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji,

A Allah ya kawar da Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu ya umarci dukan mutane a ko’ina su tuba.

A graça do arrependimento

Os que eu amo, eu repreendo e disciplino. Arrepende-te! Deus não quer que nenhum se perca — mas que todos cheguem ao arrependimento.

Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba.

Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani hallaka, sai dai kowa kai ga tuba.

Gama ba na jin daɗin mutuwar wani, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba don ku rayu!

in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.

Hezekiya ya yi Bikin Ƙetarewa

Sai Hezekiya ya aika wa dukan Isra’ila da Yahuda, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa Efraim da Manasse, yana gayyatarsu su zo haikalin Ubangiji a Urushalima, su kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, Allah na Isra’ila. Sarki da fadawansa da dukan taro a Urushalima suka yanke shawara su yi Bikin Ƙetarewa a wata na biyu. Ba su iya yinsa a daidai lokacinsa ba domin babu isashen firistocin da suka tsarkake kansu, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba. Shirin ya yi kyau ga sarki da kuma dukan taron. Suka yanke shawara su yi shelar a ko’ina a Isra’ila, daga Beyersheba zuwa Dan, suna kiran mutane su zo Urushalima, suka kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allah na Isra’ila. Ba a yi bikin da mutane masu yawa bisa ga abin da aka rubuta ba.

Bisa ga umarnin sarki, sai yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa,

"Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya. Kada ku zama kamar iyayenku da yan’uwanku, waɗanda suka yi rashin aminci ga Ubangiji Allah na kakanninsu, har ya mai da su abin tsoro, yadda kuke gani. Kada ku yi taurinkai, yadda iyayenku suka yi; ku miƙa kai ga Ubangiji. Ku zo wuri mai tsarki, wanda ya tsarkake har abada. Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin fushi mai zafi juye daga gare ku. In kuka dawo wurin Ubangiji, sa’an nan waɗanda suka kama yan’uwanku da ya’yanku za su nuna musu tausayi, su kuma dawo wannan ƙasa, gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne mai jinƙai kuma. Ba zai kau da fuskarsa daga gare ku ba, in kuka dawo gare shi."

Yan aika suka tafi gari-gari a cikin Efraim da Manasse, har zuwa Zebulun, amma mutane suka yi musu dariyar reni, suka kuma yi musu ba’a. Duk da haka, waɗansu mutanen Asher, Manasse da Zebulun suka ƙasƙantar da kansu suka tafi Urushalima. Haka ma a Yahuda, hannun Allah yana a kan mutane don ba su zuciya ɗaya su yi abin da sarki da fadawansa suka umarta, suna bin maganar Ubangiji.

Taron mutane mai girma ya haɗu a Urushalima don Bikin Burodi Marar Yisti a wata na biyu. Suka kawar da bagadai a Urushalima suka fid da bagadan turare suka zubar da su a Kwarin Kidron.

Suka yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu na wata na biyu. Firistoci da Lawiyawa suka ji kunya suka tsarkake kansu, suka kawo hadayun ƙonawa a haikalin Ubangiji. Sa’an nan suka ɗauki matsayinsu na kullum yadda yake a Dokar Musa mutumin Allah. Firistoci suka yayyafa jinin da Lawiyawa suka ba su. Da yake da yawa cikin taron ba su tsarkake kansu ba, dole Lawiyawa su yanka yan ragunan Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda ba su da tsarki, ba su kuma iya tsarkake ragunansu ga Ubangiji ba. Ko da yake yawancin mutanen da suka zo daga Efraim, Manasse, Issakar da Zebulun ba su tsarkake kansu ba, duk da haka suka ci Bikin Ƙetarewa, ba tare da bin abin da yake a rubuce ba. Amma Hezekiya ya yi addu’a dominsu cewa, "Bari Ubangiji, wanda yake nagari, gafarta wa kowa wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko da shi marar tsarki ne bisa ga dokokin wuri mai tsarki." Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya ya kuma warkar da mutane.

Isra’ilawan da suka kasance a Urushalima suka yi Bikin Burodi Marar Yisti kwana bakwai da farin ciki mai girma, yayinda Lawiyawa da firistoci suke rera ga Ubangiji kowace rana, haɗe da kayan kiɗin yabon Ubangiji.

Hezekiya ya yi magana mai ƙarfafawa ga dukan Lawiyawa waɗanda suka nuna ganewar fasaha a hidimar Ubangiji. Kwana bakwai suka ci rabonsu da aka tsara, suka miƙa hadayun salama, suka kuma yabi Ubangiji Allah na kakanninsu.

Dukan mutanen suka yarda su ƙara kwana bakwai kuma, sai suka ci gaba da bikin cikin farin ciki har waɗansu kwana bakwai kuma. Hezekiya sarkin Yahuda ya tanada bijimai dubu ɗaya da tumaki da kuma awaki dubu bakwai wa taron, fadawa kuma suka tanada musu bijimai dubu da kuma tumaki da awaki dubu goma. Firistoci masu yawa suka tsarkake kansu. Taron gaba ɗaya na Yahuda suka yi farin ciki, tare da firistoci da kuma Lawiyawa da dukan waɗanda suka taru daga Isra’ila, har ma da baƙi waɗanda suka zo daga Isra’ila da waɗanda suke zama a Yahuda. Aka yi farin ciki mai girma a Urushalima, gama tun zamanin Solomon ɗan Dawuda sarkin Isra’ila, ba a taɓa yin wani abu kamar haka a Urushalima ba. Firistoci da Lawiyawa suka tsaya suka albarkace mutane, Allah kuma ya ji su, gama addu’arsu ya kai sama, mazauninsa mai tsarki.

Ku kyakkece zuciyarku

ba rigunanku ba.

Ku juyo ga Ubangiji Allahnku,

gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma

mai jinkirin fushi da yawan ƙauna,

yakan kuma janye daga aika da bala’i.

Kira don komawa ga Ubangiji

A wata na bakwai na shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.

"Ubangiji ya yi fushi sosai da kakanninku. Saboda haka ka gaya wa mutanen, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, Ku komo gare ni,in ji Ubangiji Maɗaukaki, ni kuma zan komo gare ku,in ji Ubangiji Maɗaukaki. Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na suka ce musu, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, Ku juya daga mugayen hanyoyinku da mugayen abubuwan da kuke yi.Amma ba su saurara ba, ko ma su kula da ni, in ji Ubangiji. Yanzu ina kakanninku suke? Annabawan kuma fa, sun rayu har abada ne? Amma maganata da dokokina da na umarta ta wurin bayina annabawa fa, ashe, ba su tabbata ba a kan kakanninku?

"Sa’an nan suka tuba suka ce, Ubangiji Maɗaukaki ya yi mana daidai abin da hanyoyinmu suka cancanci mu samu, kamar dai yadda ya yi niyya yi.’ "

Mutumin a cikin itatuwan ci-zaƙi

7-8 A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato, watan Shebat, a shekara ta biyu ta Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.

Da dare, na ga wahayi, a gabana kuwa ga mutum a kan jan doki! Yana tsaye a cikin itatuwa masu furanni, a bayansa a cikin itatuwan ci-zaƙi, a bayansa kuwa akwai dawakai masu ruwan ja, ruwan ƙasa-ƙasa da kuma ruwan fari.

Sai na yi tambaya na ce, "Mene ne waɗannan ranka daɗe?"

Mala’ikan da yake magana da ni ya amsa ya ce, "Zan nuna maka mene ne su."

Sai mutumin da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin ya yi bayani cewa, "Su ne waɗanda Ubangiji ya aika ko’ina a duniya."

Sai suka ce wa mala’ikan da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin, "Mun ratsa ko’ina a duniya, sai muka ga duniya duka tana zaman lafiya."

Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya ce, "Ya Ubangiji Maɗaukaki, har yaushe za ka ci gaba da ƙi nuna wa Urushalima da kuma garuruwan Yahuda jinƙai, waɗanda kake fushi da su shekarun nan saba’in?" Sai Ubangiji ya yi wa mala’ikan da ya yi magana da ni magana da kalmomi masu daɗi da kuma masu ta’azantarwa.

Sai mala’ikan da yake magana da ni ya ce, "Ka yi shelar maganan nan, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, Ina kishi domin Urushalima da Sihiyona, amma ina fushi da ƙasashen da suke ji suna zaman lafiya, na ɗan yi fushina kawai, amma sai suka ƙara musu masifar.

"Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce, Zan komo Urushalima da jinƙai, a can ne za a sāke gina gidana. Za a kuma miƙe ma’auni a bisa Urushalima,in ji Ubangiji Maɗaukaki.

"Ci gaba da yin shela, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, Garuruwana za su sāke kwarara da wadata, Ubangiji kuma zai sāke yi wa Sihiyona ta’aziyya, kuma zaɓi Urushalima.’ "

Ƙahoni huɗu da maƙera huɗu

Sa’an nan na dubi sama a gabana kuwa sai ga ƙahoni huɗu! Na tambayi mala’ikan da yake mini magana, na ce, "Mene ne waɗannan?"

Ya amsa mini ya ce, "Waɗannan su ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda, Isra’ila da kuma Urushalima."

Sa’an nan Ubangiji ya nuna mini maƙera guda huɗu. Na yi tambaya na ce, "Mene ne waɗannan suke zuwa yi?"

Ya amsa ya ce, "Waɗannan ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda har ba wanda yake iya ɗaga kansa, amma maƙeran sun zo don su tsorata su su kuma saukar da ƙahonin ƙasashen nan waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuda don su warwatsa ta."

Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara,

amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.

Da a ce kun saurari tsawatata,

da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata

in kuma sanar da ku tunanina.

Confissão e restauração

Se confessarmos, Ele é fiel e justo. Há alegria no céu por um pecador que se arrepende — o arrependimento abre o caminho da vida.

In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.

Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasa’in da tara, waɗanda ba su bukatan tuba.

Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban mala’ikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba."

Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-