Publicidade

Bem

Por Bíblia Online

Fazer o bem é mandamento de Deus e expressão prática do amor cristão. A Bíblia convida a praticar o bem a todos, com alegria, sem se cansar — porque colheremos no tempo próprio.

Juyo daga mugunta ku yi alheri;

nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.

Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri;

yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.

Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa

zan ga alherin Ubangiji;

a ƙasar masu rai.

Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma,

gama suna nan tun .

Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata

da kuma hanyoyin tawayena;

bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni,

gama kai nagari ne, ya Ubangiji.

Ubangiji mai adalci ne cikin dukan hanyoyinsa

yana kuma nuna ƙauna ga dukan abubuwan da ya yi.

Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci

da abin da yake gaskiya, da kowace hanya mai kyau.

Abin da mutum yake sha’awa shi ne ƙauna marar ƙarewa;

gara ka zama matalauci da ka zama maƙaryaci.

Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.

Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za zama da amfani ga masu jinta.

Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.

Ƙauna

Dole ƙauna zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari.

Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.

Yancin mai bi

"Ana da dama a yi kome" sai dai ba kome ba ne yake da amfani. "Ana da dama a yi kome" sai dai ba kome ba ne mai ginawa.

Kada fa a ruɗe ku, "Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau."

Allah kuwa yana da iko ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.

Ina kuma so mata su lura su yi wa kansu adon da ya cancanta, da rigunan da suka dace, ba da adon kitso ko sa kayan zinariya ko lu’uluu ko kuma tufafi masu tsada ba, sai dai su yi ayyuka masu kyan da suka dace da matan da suke masu bauta wa Allah.

wanda ya ba da kansa dominmu don fanshe mu daga dukan mugunta kuma tsarkake wa kansa mutanen da suke nasa, waɗanda suke marmarin yin abin da yake nagari.

Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani; ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara da daurewa; ga daurewa kuwa ku ƙara da tsoron Allah; ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga yan’uwa; ga nuna alheri ga yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna.

Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta?

Ga abin da Ubangiji yana cewa,

"Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba;

ku nemi hanyoyin ,

ku tambaya inda hanyar mai kyau take, ku yi tafiya a kanta,

za ku kuwa sami hutu wa rayukanku.

Amma kun ce, Ba za mu bi ta ba.

Ubangiji nagari ne,

mafaka kuma a lokacin wahala.

Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,

Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida. Haka ma, bari haskenku haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.

Ku zama masu jinƙai, kamar yadda Ubanku mai jinƙai ne.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-