Casa de Deus
A casa de Deus é lugar de adoração, refúgio e encontro com o Sagrado. A Bíblia exalta o tabernáculo, o templo e a igreja como morada do Altíssimo entre seu povo.
A presença de Deus
Quão amáveis são os teus tabernáculos! Uma coisa pedi ao Senhor: habitar na casa do Senhor todos os dias da minha vida.
Rana guda a filayen gidan sun fi
dubu a wani wuri dabam;
zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna
da in zauna a tentunan mugaye.
Abu guda na roƙi Ubangiji,
wannan shi ne na nema,
cewa in zauna a gidan Ubangiji
dukan kwanakin raina,
in dubi kyan Ubangiji
in kuma neme shi a cikin haikalinsa.
Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa
ka kawo kusa don su zauna a filayenka!
Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka,
na haikalinka mai tsarki.
Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni,
"Bari mu tafi gidan Ubangiji."
Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi
dukan kwanakin raina,
zan kuwa zauna a gidan Ubangiji
har abada.
Amma ni kamar itace zaitun ne
ina haɓaka a gidan Allah;
na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah
har abada abadin.
gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata,
kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina.
O templo
Minha casa será chamada casa de oração. O zelo da tua casa me consumiu. O verdadeiro templo é o corpo do cristão.
Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai. Ya ce musu, "A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan addu’a,’ amma kuna mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ "
Da lokacin Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima. A filin haikali ya sami mutane suna sayar da shanu, tumaki da tattabaru, waɗansu kuma zaune a tebur suna canjin kuɗi. Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu. Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, "Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!" Sai almajiransa suka tuna cewa a rubuce yake, "Himma saboda gidanka zai cinye ni."
Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne;
in na yi jinkiri, za ka san yadda ya kamata mutane su tafiyar da halayensu a cikin jama’ar Allah, wadda take ikkilisiyar Allah rayayye, ginshiƙi da kuma tushen gaskiya.
Amma Kiristi mai aminci ne kamar ɗa a gidan Allah. Mu kuwa gidansa ne, in muka tsaya gabanmu gadi da kuma begen da muke taƙama a kai.
"Kakanni-kakanninmu suna da tabanakul na Shaida tare da su a hamada. An yi shi bisa ga yadda Allah ya umarci Musa, bisa ga zānen da ya gani. Bayan sun gāji tabanakul nan, kakanninmu a ƙarƙashin jagorancin Yoshuwa suka kawo shi tare da su, lokacin da suka ƙwace ƙasar daga al’umman da Allah ya kora a idanunsu. Tabanakul ɗin ya kasance a ƙasar har zamanin Dawuda, wanda ya sami tagomashi daga Allah, ya kuma nemi yă yi wa Allah na Yaƙub wurin zama. Amma Solomon ne ya gina masa gida.
"Duk da haka, Mafi Ɗaukaka ba ya zama a gidajen da mutane suka gina. Kamar yadda annabi ya faɗi cewa,
" ‘Sama ne kursiyina,
duniya kuma wurin ajiye tafin ƙafata.
Wane irin gida za ka gina mini?
Ko kuwa ina wurin hutuna zai kasance?
In ji Ubangiji.
Ba hannuna ne ya yi dukan waɗannan abubuwa ba?’. 2
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
"Sama kursiyina ce,
duniya kuma matashin sawuna.
Ina gidan da za ku gina mini?
Ina wurin hutuna zai kasance?
Ba hannuna ba ne ya yi dukan waɗannan abubuwa,
ta haka suka kasance?"
In ji Ubangiji.
"Wannan mutum ne nake jin daɗi,
shi da yake mai ƙasƙanci da kuma zuciyar yin tuba,
yana kuma rawar jiki ga maganata.
Sa’ad da Yaƙub ya farka daga barci, sai ya yi tunani ya ce, "Tabbatacce Ubangiji yana a wannan wuri, ban kuwa sani ba." Ya ji tsoro, ya kuma ce, "Wane irin wuri ne mai banrazana haka! Lalle wannan gidan Allah ne, kuma nan ne ƙofar sama."