Publicidade

Cânticos 4

Ƙaunatacce

1 Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata!

Kai, ke kyakkyawa ce!

Idanunki sun yi kamar na kurciya a cikin lulluɓinki.

Gashinki ya yi kamar garken awaki

da suke gangarawa daga Dutsen Gileyad.

2 Haƙoranki sun yi kamar garken tumakin da ba a daɗe da yin musu sausaya ba,

da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka.

Kowanne yana tare da ɗan’uwansa;

babu waninsu da yake shi kaɗai.

3 Leɓunanki kamar zaren jan garura

bakinki yana da kyau.

Kumatunki sun yi kamar rumman

da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki.

4 Wuyanki ya yi kamar hasumiyar Dawuda,

da aka gina da daraja;

a kansa an rataye garkuwoyi dubu,

dukansu garkuwoyin jarumawa ne.

5 Nonanki biyu sun yi kamar bareyi biyu,

kamar tagwayen barewa

da suke kiwo a cikin furen bi-rana.

6 Sai gari ya waye

inuwa kuma ta watse,

zan je dutsen mur

da kuma tudun turare.

7 Duk, ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata;

babu wani lahani a cikinki.

8 Ki tare da ni daga Lebanon, amaryata,

zo tare da ni daga Lebanon.

Ki gangara daga ƙwanƙolin Amana,

daga ƙwanƙolin Senir, ƙwanƙolin Hermon,

daga ramin zaki

da kuma dutsen da damisoshi suke zama.

9 Kin saci zuciyata, ’yar’uwata, amaryata;

kin saci zuciyata

da hararar idanunki,

da dutse mai daraja guda na abin wuyanki.

10 Ƙaunarki abar farin ciki ne, ’yar’uwata, amaryata!

Ƙaunarki ta fi ruwan inabi gamsuwa,

ƙanshin turarenki kuma ya fi duk wani kayan yaji!

11 Leɓunanki suna zub da zaƙi kamar kakin zuma, amaryata;

madara da zuma suna a ƙarƙashin harshenki.

Ƙanshin rigunanki ya yi kamar na Lebanon.

12 Ke lambu ne da aka kulle, ’yar’uwata, amaryata;

ke maɓulɓula ce da aka kewaye, maɓulɓular da aka rufe.

13 Shuke-shukenki gonar rumman ne

da ’ya’yan itace masu kyau

na lalle da nardi,

14 nardi, da asfaran,

kalamus, da kirfa,

da kowane irin itacen turare,

da mur da aloyes

da kuma dukan kayan yaji masu kyau.

15 Ke lambun maɓulɓula ne,

rijiya mai ruwan da yake gudu

yana gangarawa daga Lebanon.

Ƙaunatacciya

16 Farka, iskar arewa,

ki kuma zo, iskar kudu!

Hura a kan lambuna,

don ƙanshinsa yă bazu har waje.

Bari ƙaunataccena yă zo cikin lambunsa

yă ɗanɗana ’ya’yan itacensa mafi kyau.

Veja também

Publicidade
Cânticos
Ver todos os capítulos de Cânticos
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_18-40-07-