Pular para o conteúdo
Publicidade

Waƙar Waƙoƙi 6

Ƙawaye

1 Ina ƙaunataccenki ya tafi,

yake mafiya kyau cikin mata?

Wace hanya ce ƙaunataccenki ya bi,

don mu taimake ki nemansa.

Ƙaunatacciya

2 Ƙaunataccena ya gangara zuwa lambunsa,

zuwa inda fangulan kayan yaji suke,

don yi kiwo a cikin lambun

don kuma tattara furen bi-rana.

3 Ni na ƙaunataccena ce, ƙaunataccena kuma nawa ne;

yana kiwo a cikin furen bi-rana.

Ƙaunatacce

4 Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza,

kyakkyawa kuma kamar Urushalima,

mai daraja kamar mayaƙa da tutoti.

5 Ki kau da idanu daga gare ni;

gama suna rinjayata.

Gashinki yana kama da garken awakin

da suke gangarawa daga Gileyad.

6 Haƙoranki suna kama da garken tumakin

da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka.

Kowanne yana tare da ɗan’uwansa;

babu waninsu da yake shi kaɗai.

7 Kumatunki sun yi kamar rumman

da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki.

8 Sarauniyoyi sittin za su iya kasance a can,

da ƙwarƙwarai tamanin

da kuma budurwai da suka wuce ƙirge;

9 amma kurciyata, cikakkiyata, dabam take,

tilo kuwa ga mahaifiyarta,

yar lele ga wadda ta haife ta.

Yan mata sun gan ta suka ce da ita mai albarka;

sarauniyoyi da ƙwarƙwarai sun yabe ta.

Ƙawaye

10 Wace ce wannan da ta bayyana sai ka ce ketowar alfijir?

Kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana,

mai daraja kamar taurari a jere?

Ƙaunatacce

11 Na gangara zuwa cikin itatuwan almon

don in ga ƙananan itatuwan da suke girma a kwari,

don in ga ko inabi sun yi ya’ya

ko rumman suna fid da furanni.

12 Kafin in san wani abu,

sha’awarta ta sa ni a cikin keken yaƙin sarkin mutanena.6.12 Ko kuwa cikin keken yaƙin Amminadab; Ko kuwa cikin keken yaƙin mutanen sarki

Ƙawaye

13 Ki dawo, ki dawo, ya Bashulammiya;

ki dawo, ki dawo, don mu dube ki!

Ƙaunatacce

Don me kuke duban Bashulammiya

sai ka ce rawar Mahanayim?

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também