1 Waƙar Waƙoƙin Solomon.
2 Bari yă sumbace ni da sumbar bakinsa,
gama ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi.
3 Ƙanshin turarenka mai daɗi ne;
sunanka kuwa kamar turaren da aka tsiyaye ne.
Shi ya sa mata suke ƙaunarka!
4 Ka ɗauke ni mu gudu, mu yi sauri!
Bari sarki yă kai ni gidansa.
Muna farin ciki muna kuma murna tare da kai,
za mu yabi ƙaunarka fiye da ruwan inabi.
Daidai ne su girmama ka!
5 Ni baƙa ce, duk da haka kyakkyawa.
Ya ku ’yan matan Urushalima,
ni baƙa ce kamar tentunan Kedar,
kamar labulen tentin Solomon.
6 Kada ku harare ni domin ni baƙa ce,
gama rana ta dafa ni na yi baƙa.
’Ya’yan mahaifiyata maza sun yi fushi da ni
suka sa ni aiki a gonakin inabi;
na ƙyale gonar inabi na kaina.
7 Faɗa mini, kai da nake ƙauna, ina kake kiwon garkenka
kuma ina kake kai tumakinka su huta da tsakar rana.
Me ya sa zan kasance kamar macen da aka lulluɓe
kusa da garkunan abokanka?
8 Ke mafiya kyau a cikin mata, in ba ki sani ba,
to, ki dai bi labin da tumaki suke bi
ki yi kiwon ’yan awakinki
kusa da tentunan makiyaya.
9 Ina kwatanta ke ƙaunatacciyata, da goɗiya
mai jan keken yaƙin kayan Fir’auna.
10 ’Yan kunne sun ƙara wa kumatunki kyau,
wuyanki yana da jerin kayan wuya masu daraja.
11 Za mu yi ’yan kunnenki na zinariya,
da adon azurfa.
12 Yayinda sarki yake a teburinsa,
turarena ya bazu da ƙanshi.
13 Ƙaunataccena yana kamar ƙanshin mur a gare ni,
kwance a tsakanin ƙirjina.
14 Ƙaunataccena kamar tarin furanni jeji ne gare ni
daga gonakin inabin En Gedi.
15 Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata!
Kai, ke kyakkyawa ce!
Idanunki kamar na kurciya ne.
16 Kai kyakkyawa ne, ƙaunataccena!
Kai, kana ɗaukan hankali!
Gadonmu koriyar ciyawa ce.
17 Al’ul su ne ginshiƙan gidanmu;
fir su ne katakan rufin gidanmu.