Pular para o conteúdo
Publicidade

Casal

Por Bíblia Online

O casal cristão é parceria abençoada por Deus. Juntos são mais fortes. O amor mutual, a paciência e a submissão ao Senhor são os pilares do casamento que honra a Deus.

Unidos em Cristo

Eu e minha casa serviremos ao Senhor. O vínculo perfeito é o amor que tudo suporta e tudo espera.

Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa."

Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.

Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

Ku bar salamar Kiristi yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.

Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

Ku tabbata cewa kada kowa rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.

Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum raba."

Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum raba."

O projeto divino

Não é bom que o homem esteja só. Dois são melhores do que um — e o cordão de três dobras não se rompe facilmente.

Ubangiji Allah ya ce, "Bai yi kyau mutumin kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi."

Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

Mutumin da matarsa, dukansu biyu tsirara suke, ba su kuwa ji kunya ba.

Sa’an nan Allah ya ce, "Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa."

Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.

Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.

Miji da mace ya halicce su.

Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, "Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa."

Amma ku, ku yi ta haihuwa, ku ƙaru; ku yaɗu a duniya, ku yi yawa a bisanta."

Biyu sun fi ɗaya,

gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.

Ashe, Ubangiji bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman ya’ya masu tsoron Allah. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka.

Amor conjugal

Maridos, amai vossas mulheres. A mulher virtuosa é achada de Deus. Cresçam juntos em graça e verdade.

Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta.

Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne. Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai ciyar da shi, kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya,

"Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya."

Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.

Saboda haka dole kowannenku bar yin ƙarya, kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne. "Cikin fushinku kada ku yi zunubi." Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi, kada kuma ku ba wa Iblis dama. Duk wanda yake sata, sai daina sata, dole kuma yi aiki, yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don sami abin da zai iya raba da masu bukata.

Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za zama da amfani ga masu jinta. Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa. Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.

Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau

ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.

Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku. Bai kamata kowannenku kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai kula da sha’anin waɗansu ma.

Dukanku ya’yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Gama dukanku da aka yi muku baftisma cikin Kiristi, kuna sanye da Kiristi ke nan. Babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, bawa da yantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu.

Aure zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.

Kada ku haɗa kai da marasa bi

Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu?

Duk da haka a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, namiji kuma ba a rabe yake da mace ba.

Seja o primeiro