Publicidade

A comunhão

Por Bíblia Online

A comunhão cristã é dom e mandamento. Juntos somos mais fortes. A Bíblia celebra a unidade dos crentes em Cristo como antecipação do céu na terra.

Ni a cikinsu kai kuma a cikina. Bari su kasance da cikakken haɗinkai, domin duniya ta san cewa kai ka aiko ni. Ka kuwa ƙaunace su yadda ka ƙaunace ni.

"Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna. Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna."

Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare. Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa. Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya, suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.

Muna yin muku shelar abin da muka gani, muka kuma ji ne, domin ku ma ku yi zumunci tare da mu. Zumuncinmu kuwa yana tare da Uba da kuma Ɗansa, Yesu Kiristi.

Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin yan’uwanmu.

Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.

wato, don ni da ku mu ƙarfafa juna ta wurin bangaskiyarmu.

Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna, tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba.

Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe

haka mutum kan koyi daga mutum.

Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi.

Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.

Biyu sun fi ɗaya,

gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.

In ɗaya ya fāɗi,

abokinsa zai taimake shi tashi.

Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi

ba shi kuma da wanda zai taimake shi tashi!

In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna.

Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai?

Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya,

mutum biyu za su iya kāre kansu.

Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.

Seja o primeiro
Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-29_22-07-56-