Coração puro
Bem-aventurados os puros de coração, porque verão a Deus. A pureza de coração é alvo, privilégio e busca constante do cristão que deseja contemplar a face do Senhor.
Coração puro
Bem-aventurados os puros de coração. A pureza interior precede toda transformação externa e abre os olhos para ver a Deus.
Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya,
gama za su ga Allah.
Wa zai iya hawan tudun Ubangiji?
Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?
Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya,
wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki
ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.
Zai sami albarka daga Ubangiji
da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.
Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina
ka kuma shafe dukan kurakuraina.
Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah,
ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina.
Kada ka fid da ni daga gabanka
ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni.
Tabbatacce Allah mai alheri ne ga Isra’ila,
ga waɗanda suke masu tsabta a zuciya.
Purificar-se
Todo o que tem essa esperança em Cristo se purifica. O amor procede de coração puro, boa consciência e fé sincera.
Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.
Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake. Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.
Maƙasudin wannan umarnin dai ƙauna ce, wadda take zuwa daga zuciya mai tsabta da lamiri mai kyau da kuma sahihiyar bangaskiya.
Ka yi nesa da mugayen sha’awace-sha’awace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta.
Addu’ata ita ce ƙaunarku tă yi ta cin gaba da ƙaruwa cikin sani da kuma zurfin ganewa, don ku iya rarrabe abin da yake mafi kyau, ku kuma zama da tsarki, marasa aibi har yă zuwa ranar Kiristi, cikakku da sakamakon aikin adalci da yake zuwa ta wurin Yesu Kiristi, zuwa ga ɗaukakar Allah da kuma yabonsa.
Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba, don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba.
Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya.
Dukan hanyoyin mutum sukan yi kamar marar laifi ne gare shi,
amma Ubangiji yakan auna manufofi.