Publicidade

Joel 1

1 Maganar Ubangiji wadda ta zo wurin Yowel ɗan Fetuwel.

Mamayar da fāra ta yi

2 Ku ji wannan, ku dattawa,

ku kasa kunne, dukan waɗanda suke zaune a ƙasar.

Ko wani abu makamancin haka ya taɓa faruwa a kwanakinku

ko a kwanakin kakanninku?

3 Ku faɗa wa ’ya’yanku,

bari kuma ’ya’yanku su faɗa wa ’ya’yansu,

’ya’yansu kuma su faɗa wa tsara ta gaba.

4 Abin da ɗango ya bari

fāri masu girma sun cinye;

abin da fāri masu girma suka bari,

burduduwa ta cinye;

abin da burduduwa ta bari sauran kwari sun cinye.

5 Ku farka, ku bugaggu, ku yi kuka!

Ku yi kuka da ƙarfi, ku dukan mashayan ruwan inabi;

ku yi kuka mai ƙarfi saboda sabon ruwan inabi,

gama an riga an ƙwace ta daga leɓunanku.

6 Wata al’umma ta mamaye ƙasata,

tana da ƙarfi ba ta kuma ƙidayuwa;

tana da haƙoran zaki,

da zagar zakanya.

7 Ta mayar da kuringar inabina kango

ta kuma lalatar da itatuwan ɓaurena.

Ta ɓamɓare bayansu duka

ta kuma jefar da su

ta bar rassansu fari fat.

8 Ku yi makoki kamar budurwa

a cikin tsummoki

tana baƙin ciki domin mijinta na ƙuruciyarta.

9 Hadayun hatsi da hadayun sha

an yanke su daga gidan Ubangiji.

Firistoci suna makoki,

su waɗanda suke yi wa Ubangiji hidima.

10 Filaye sun zama marasa amfani,

ƙasa ta bushe;

an lalatar da hatsi,

sabon ruwan inabin ya bushe,

mai kuma ba amfani.

11 Ku fid da zuciya, ku manoma,

ku yi ihu, ku masu noma inabi;

ku yi baƙin ciki saboda alkama da sha’ir,

saboda an lalata girbin filaye.

12 Kuringar inabin ta bushe

itacen ɓaure kuma ya yi yaushi,

’ya’yan rumman, itacen dabino da itacen gawasa,

dukan itatuwan filaye, sun bushe.

Tabbatacce farin cikin ’yan adam

ya bushe.

Kira don makoki

13 Ku sa tsummoki, ya firistoci, ku yi makoki;

ku yi ihu, ku da kuke yin hidima a gaban bagade.

Zo, ku kwana saye da tsummoki,

ku waɗanda kuke yi wa Allahna hidima,

gama an yanke hadayun hatsi da hadayun sha

daga gidan Allahnku.

14 Ku yi shelar azumi mai tsarki;

ku kira tsarkakan taro.

Ku kira dattawa

da kuma dukan mazaunan ƙasar

zuwa gidan Ubangiji Allahnku,

ku kuma yi kuka ga Ubangiji.

15 Kaito saboda wannan rana!

Gama ranar Ubangiji ta kusa,

za tă zo kamar hallaka daga wurin Maɗaukaki.

16 Ba a yanke abinci

a idanunmu,

farin ciki da kuma murna

daga gidan Allahnmu ba?

17 Iri suna ta yanƙwanewa

a busasshiyar ƙasa

Ɗakunan ajiya sun lalace,

an rurrushe rumbunan hatsin,

gama hatsi ya ƙare.

18 Ji yadda dabbobi suke nishi!

Garkunan shanu sun ruɗe

saboda ba su da ciyawa,

har garkunan tumaki ma suna shan wahala.

19 A gare ka, ya Ubangiji, nake kira,

gama wuta ta cinye wurin kiwo

harshen wuta kuma ya ƙone dukan itatuwan jeji.

20 Har ma namun jeji suna haki gare ka;

rafuffuka sun bushe

wuta kuma ta cinye wurin kiwo a jeji.

Veja também

Publicidade
Joel
Ver todos os capítulos de Joel
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-