Pular para o conteúdo
Publicidade

Hosiya 14

Tuba don kawo albarka

1 Ku dawo, ya Isra’ila, ga Ubangiji Allahnku.

Zunubanku ne sun zama sanadin fāɗuwarku!

2 Ku ɗauki magana tare da ku

ku komo wurin Ubangiji.

Ku ce masa,

"Ka gafarta mana dukan zunubanmu

ka kuma karɓe mu da alheri,

don mu iya yabe ka da leɓunanmu.14.2 Ko kuwa miƙa leɓunanmu kamar hadayun bijimai

3 Assuriya ba za su iya cece mu ba;

ba za mu hau dawakan yaƙi ba.

Ba za mu ƙara ce, Allolinmu

wa abin da hannuwanmu suka yi ba,

gama a gare ka ne maraya yakan sami jinƙai."

4 "Zan gyara ɓatancinsu

in kuma ƙaunace su a sake,

gama fushina ya juya daga gare su.

5 Zan zama kamar raɓa ga Isra’ila

zai yi fure kamar lili.

Kamar al’ul na Lebanon

zai sa saiwarsa zuwa ƙasa;

6 tohonsa za su yi girma.

Darajarsa za zama kamar itacen zaitun,

ƙanshinsa kamar al’ul na Lebanon.

7 Mutane za su sāke zauna a inuwarsa.

Zai haɓaka kamar ƙwayar hatsi.

Zai yi fure kamar kuringa,

zai zama sananne kamar ruwan inabi daga Lebanon.

8 Efraim zai ce, me kuma zai haɗa ni da gumaka?

Zan amsa masa in kuma lura da shi.

Ni kamar koren itacen fir ne;

amincinka yana fitowa daga gare ni ne."

9 Wane ne yake da hikima? Zai gane waɗannan abubuwa.

Hanyoyin Ubangiji daidai ne;

masu adalci sukan yi tafiya a kansu,

amma yan tawaye sukan yi tuntuɓe a kansu.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também