Pular para o conteúdo
Publicidade

Hosiya 12

1 Efraim yana kiwo a kan iska;

yana fafarar iskar gabas dukan yini

yana riɓaɓɓanya ƙarairayi da rikici.

Ya yi yarjejjeniya da Assuriya

ya kuma aika wa Masar man zaitun.

2 Ubangiji yana da ƙarar da zai kawo a kan Yahuda;

zai hukunta Yaƙub bisa ga hanyoyinsa

zai sāka masa bisa ga ayyukansa.

3 A cikin mahaifa ya cafke ɗiɗɗigen ɗan’uwansa;

a matsayin mutum ya yi kokawa da Allah.

4 Ya yi kokawa da mala’ika ya kuma rinjaye shi;

ya yi kuka ya kuma yi roƙo don tagomashi.

Ya same shi a Betel

ya kuma yi magana da shi a can,

5 Ubangiji Allah Maɗaukaki,

Ubangiji ne sunansa sananne!

6 Amma dole ku koma ga Allahnku;

ku ci gaba da ƙauna da yin gaskiya,

ku kuma saurari Allahnku kullum.

7 Ɗan kasuwa yana amfani da mudu marar gaskiya;

yana jin daɗin cuta.

8 Efraim yana fariya yana cewa,

"Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta.

Da dukan wadatata ba za a sami

wani laifi ko zunubi a gare ni ba."

9 "Ni ne Ubangiji Allahnku,

wanda ya fitar da ku daga12.9 Ko kuwa Allah / tun kuna cikin Masar;

zan sa ku sāke zauna a tentuna,

kamar a kwanakin ƙayyadaddun bukukkuwanku.

10 Na yi magana da annabawa,

na ba su wahayi da yawa

na kuma ba da misalai ta wurinsu."

11 Gileyad mugu ne?

Mutanensa mutanen banza ne!

Suna miƙa bijimai a Gilgal?

Bagadansu za su zama tsibin duwatsu.

A gonar da aka nome.

12 Yaƙub ya gudu zuwa ƙasar Aram;12.12 Wato, Arewa maso yamma Mesofotamiya

Isra’ila ya yi bauta don sami mata,

domin kuma biya, sai da ya yi kiwon tumaki.

13 Ubangiji ya yi amfani da annabi don fitar da Isra’ila daga Masar

ta wurin annabi ya lura da shi.

14 Amma Efraim ya yi muguwar tsokana da ta sa ya yi fushi;

shugabansa zai ɗora musu hakkin jini a kansa

kuma zai sāka masa saboda wulaƙancinsa.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também