Publicidade

Salmos 8

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Zabura ta Dawuda.

1 Ya Ubangiji, shugabanmu,

sunanka da girma take a cikin dukan duniya!

Ka kafa ɗaukakarka

bisa sammai.

2 Daga leɓunan yara da jarirai

ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka

da masu ɗaukan fansa su yi shiru.

3 Sa’ad da na dubi sammai,

aikin yatsotsinka,

wata da taurari

waɗanda ka ajiye a wurarensu,

4 wane ne mutum da kake tunawa da shi,

ɗan mutum da kake lura da shi?

5 Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah

ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.

6 Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka;

ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,

7 dukan shanu da tumaki,

da kuma namun jeji,

8 tsuntsayen sararin sama

da kifin teku,

da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.

9 Ya Ubangiji, shugabanmu,

sunanka da girma take a cikin dukan duniya!

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-15_21-32-39-