Publicidade

Salmos 129

Waƙar haurawa.

1 Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami,

bari Isra’ila yă ce,

2 sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami,

amma ba su yi nasara a kaina ba.

3 Manoma sun nome bayana

suka yi kunyoyinsu da tsayi.

4 Amma Ubangiji mai adalci ne;

ya ’yantar da ni daga igiyoyin mugaye.

5 Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona

a juye da su baya da kunya.

6 Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi,

wadda takan bushe kafin tă yi girma;

7 da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa,

balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.

8 Kada masu wuce su ce,

"Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku;

muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji."

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_06-50-08-