Publicidade

Salmos 125

Waƙar haurawa.

1 Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona,

wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada.

2 Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima,

haka Ubangiji ya kewaye mutanensa

yanzu da har abada kuma.

3 Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasance

a kan ƙasar da take rabon adalai ba,

domin kada masu adalci su yi amfani

da hannuwansu su aikata mugunta.

4 Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu,

ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu.

5 Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi

Ubangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta.

Salama tă kasance tare da Isra’ila.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-