Publicidade

Salmos 96

1 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji;

ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.

2 Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa;

ku yi shelar cetonsa kowace rana.

3 Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,

manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.

4 Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo;

tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.

5 Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne,

amma Ubangiji ne ya yi sammai.

6 Daraja da ɗaukaka suna a gabansa;

ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa.

7 Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai

ku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi.

8 Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa;

ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa.

9 Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa;

ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya.

10 Ku faɗa cikin al’ummai, "Ubangiji yana mulki."

Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba;

zai yi wa mutane hukunci da gaskiya.

11 Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;

bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa;

12 bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu.

Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki;

13 za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa,

yana zuwa don yă hukunta duniya.

Zai hukunta duniya cikin adalci

mutane kuma cikin amincinsa.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_18-40-07-