Publicidade

Salmos 133

Waƙar haurawa. Ta Dawuda.

1 Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma

sa’ad da ’yan’uwa suna zaman lafiya!

2 Yana kamar mai mai darajar da aka zuba a kai,

yana gangarawa a gemu,

yana gangarawa a gemun Haruna,

har zuwa wuyan rigunansa.

3 Yana kamar raɓar Hermon

da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona.

Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa,

har ma rai na har abada.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-