Publicidade

Salmos 67

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura. Waƙa.

1 Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu

yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, Sela

2 don a san hanyoyinka a duniya,

cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.

3 Bari mutane su yabe ka, ya Allah;

bari dukan mutane su yabe ka.

4 Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki,

gama kana mulkin mutanenka da adalci

kana kuma bi da al’umman duniya. Sela

5 Bari mutane su yabe ka, ya Allah;

bari dukan mutane su yabe.

6 Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta

Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.

7 Allah yă sa mana albarka,

dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_06-50-08-