Publicidade

Salmos 11

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don busa. Ta Dawuda.

1 A wurin Ubangiji ne nake samun mafaka.

Yaya za ku ce mini,

"Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu.

2 Gama duba, mugaye sun tanƙware bakkunansu;

sun kuma ɗana kibiyoyinsu

don su harbi mutanen kirki a zuciya

daga cikin duhu.

3 Sa’ad da aka tumɓuke tushe,

me adali zai iya yi?"

4 Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki;

Ubangiji yana a kursiyinsa a sama.

Yana kallon ’ya’yan mutane;

idanunsa suna bincike su.

5 Ubangiji yana bincike adalai,

amma ransa yana ƙi mugaye

da masu son rikici.

6 A kan mugaye zai zuba

garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu;

iska mai zafi zai zama rabonsu.

7 Gama Ubangiji mai adalci ne,

yana ƙaunar gaskiya

masu adalci za su ga fuskarsa.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_06-50-08-