Publicidade

Salmos 114

1 Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar,

gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe,

2 Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah,

Isra’ila mallakarsa.

3 Teku ya kalla ya kuma gudu,

Urdun ya juye da baya;

4 duwatsu suka yi tsalle kamar raguna,

tuddai kamar tumaki.

5 Me ya sa, ya teku, kika gudu,

Ya Urdun, ka juya baya,

6 ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna,

ku tuddai, kamar tumaki?

7 Ki yi rawar jiki, ya duniya, a gaban Ubangiji,

a gaban Allah na Yaƙub,

8 wanda ya juye dutse ya zama tafki,

dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓulan ruwa.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-22_10-02-25-