Publicidade

Lamentações 3

1 Ni ne mutumin da ya ga azaba

ta wurin bulalar fushin Ubangiji.

2 Ya kore ni, ya sa na yi tafiya

a cikin duhu maimakon a cikin haske;

3 ba shakka, ya juya mini baya, yana gāba da ni

sau da sau, dukan yini.

4 Ya sa fatar jikina da naman jikina sun tsufa

ya kuma karya ƙasusuwana.

5 Ya yi mini kwanton ɓauna ya kuma kewaye ni

da baƙin ciki da kuma wahala.

6 Ya sa na zauna a cikin duhu

kamar waɗanda suka mutu da jimawa.

7 Ya kewaye ni yadda ba zan iya gudu ba;

Ya daure ni da sarƙa mai nauyi.

8 Ko lokacin da nake kira don neman taimako,

ba ya jin addu’ata.

9 Ya tare hanyata da tubula na duwatsu;

ya sa hanyata ta karkace.

10 Kamar beyar da take a laɓe tana jira,

kamar zaki a ɓoye,

11 ya janye ni daga kan hanya ya ɓatar da ni

ya bar ni ba taimako.

12 Ya ja kwarinsa

ya sa in zama abin baratarsa.

13 Ya harbi zuciyata

da kibiyoyin kwarinsa.

14 Na zama abin dariya ga mutanena duka;

suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini.

15 Ya cika ni da kayan ɗaci

ya gundure ni da abinci mai ɗaci.

16 Ya kakkarya haƙorana da tsakuwa;

ya tattake ni cikin ƙura.

17 An hana ni salama;

na manta da ko mene ne ake kira wadata.

18 Saboda haka na ce, "Darajata ta ƙare

da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji."

19 Na tuna da azabata da kuma sintiri,

da na yi ta yi da ɗacin rai.

20 Na tuna su sosai,

sai kuma na ji ba daɗi a raina.

21 Duk da haka na tuna da wannan

na kuma sa bege ga nan gaba.

22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;

gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.

23 Sababbi ne kowace safiya;

amincinka kuwa mai girma ne.

24 Na ce wa kaina, "Ubangiji shi ne nawa;

saboda haka zan jira shi."

25 Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa,

ga kuma wanda yake neman shi;

26 yana da kyau ka jira shiru

domin samun ceton Ubangiji.

27 Yana da kyau mutum yă sha wuya

tun yana yaro.

28 Bari yă zauna shiru shi kaɗai,

gama haka Ubangiji ya sa yă yi.

29 Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙura

kila akwai bege.

30 Bari yă ba da kumatunsa a mare shi,

yă kuma bari a ci masa mutunci.

31 Gama Ubangiji ba ya

yashe mutane har abada.

32 Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai,

ƙaunarsa tana da yawa.

33 Gama ba haka kawai yake kawo wahala

ko ɓacin rai ga ’yan adam ba.

34 Bai yarda a tattake

’yan kurkuku a ƙasa ba,

35 ko kuma a danne wa mutum hakkinsa

a gaban Maɗaukaki,

36 ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya

ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba?

37 Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika

in ba Ubangiji ne ya umarta ba?

38 Ba daga bakin Maɗaukaki ne

bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba?

39 Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni

sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa?

40 Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta,

sai mu kuma koma ga Ubangiji.

41 Bari mu ɗaga zuciyarmu da hannuwanmu

ga Allah na cikin sama, mu ce,

42 "Mun yi zunubi mun yi tawaye

ba ka kuwa gafarta ba.

43 "Ka rufe kanka da fushi, ka fafare mu;

ka karkashe mu ba tausayi.

44 Ka rufe kanka da gajimare

don kada addu’armu ta kai wurinka.

45 Ka mai da mu tarkace da juji

a cikin mutane.

46 "Dukan maƙiyanmu suna ta yin mana magana

marar daɗi.

47 Muna cika da tsoro,

da lalatarwa da hallakarwa."

48 Hawaye na kwararowa daga idanuna

domin an hallaka mutanena.

49 Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye,

ba hutawa.

50 Har sai in Ubangiji ya duba

daga sama ya gani.

51 Abin da nake gani yana kawo mini baƙin ciki

domin dukan matan birnina.

52 Maƙiyana suna farauta ta

ba dalili kamar tsuntsu.

53 Sun yi ƙoƙari su kashe ni a cikin rami

suka kuma jajjefe ni da duwatsu;

54 ruwaye suka rufe kaina,

sai na yi tunani cewa na kusa mutuwa.

55 Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji,

daga rami mai zurfi.

56 Ka ji roƙona, "Kada ka toshe kunnuwanka

ka ƙi jin roƙona na neman taimako."

57 Ka zo kusa lokacin da na kira ka,

kuma ka ce mini, "Kada ka ji tsoro."

58 Ya Ubangiji, ka goyi bayana;

ka fanshi raina.

59 Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba.

Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya!

60 Ka ga zurfin ramakonsu,

da duk mugun shirin da suke yi mini.

61 Ya Ubangiji, ka ji zaginsu,

da duka mugun shirin da suke yi mini

62 Abin da maƙiyana suke yin raɗa a kai

game da ni duk yini.

63 Dube su! A zaune ko a tsaye,

suna yi mini ba’a cikin waƙoƙinsu.

64 Ka ba su abin da ya dace su samu, ya Ubangiji,

domin abin da hannuwansu suka yi.

65 Ka sa yana ta rufe zuciyarsu,

kuma bari la’anarka ta bi su.

66 Ka fafare su cikin fushi

ka hallaka su daga cikin duniya ta Ubangiji.

Veja também

Publicidade
Lamentações
Ver todos os capítulos de Lamentações
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-