Publicidade

Lamentações 1

1 Yanzu birnin ya zama babu kowa a ciki,

birnin da a dā yake cike da mutane!

Yanzu birnin ya zama kamar gwauruwa,

wadda a dā babba ce ita a cikin ƙasashe!

Ita da take sarauniya a cikin larduna

yanzu ta zama baiwa.

2 Tana yin kuka mai zafi da dare,

hawaye na gangara a kan kumatunta.

A cikin masoyanta duka

babu wanda ya yi mata ta’aziyya.

Duk abokanta sun yashe ta;

sun zama abokan gābanta.

3 Bayan wahala da baƙin ciki,

Yahuda ta tafi bauta.

Ta zauna a cikin ƙasashe,

ba tă samu wurin hutawa ba.

Duk masu fafararta sun same ta

sa’ad da take cikin matuƙar ɓacin rai.

4 Hanyoyin zuwa Sihiyona suna makoki,

gama ba wanda ya zo bikin da ta shirya.

Ba kowa a hanyoyin shiganta.

Firistocinta suna gurnani,

’yan matana kuma suna wahala,

kuma tana cikin shan wahala ƙwarai.

5 Maƙiyanta sun zama shugabanninta;

Abokan gābanta suna da kwanciyar rai.

Ubangiji ya kawo mata ɓacin rai

domin yawan zunubanta.

’Ya’yanta sun tafi bauta,

a ƙarƙashin maƙiyanta.

6 Diyar Sihiyona ba ta

da sauran daraja.

’Ya’yan sarakunanta sun zama kamar bareyi

waɗanda suka rasa wurin kiwo;

cikin rashin ƙarfi suka guje

wa masu fafararsu.

7 A cikin kwanakin da take shan wahala take kuma yawo

Urushalima ta tuna da dukan dukiyar

da take da ita a kwanakin dā can.

Sa’ad da mutanenta suka faɗa cikin hannun abokan gābanta,

ba wanda ya taimake ta.

Maƙiyanta suka dube ta

suka yi mata dariya don hallakar da ta auko mata.

8 Urushalima ta yi zunubi ƙwarai

saboda haka ta zama marar tsarki.

Dukan masu martaba ta sun raina ta,

gama sun ga tsiraicinta;

ita ma da kanta tana nishi da ƙyar

ta kuma juya baya.

9 Ƙazantarta ta manne wa rigunanta;

ba tă kula da nan gaba ba,

fāɗuwarta kuwa babban abu ne;

babu wanda zai yi mata ta’aziyya.

"Duba, ya Ubangiji, ka ga wahalata,

gama maƙiyi ya yi nasara."

10 Maƙiya ya kwashe

dukiyarta duka;

ta ga mutanen da ba su san Allah ba

sun shiga wuri mai tsarkinta

waɗanda ka hana su

shiga taron jama’arka.

11 Dukan mutanenta suna nishi

da ƙyar suna neman burodi;

sun sayar da dukiyarsu don su samu abinci

don kada su mutu da yunwa.

"Ubangiji, ka duba ka gani,

gama an yashe ni."

12 "Ko wannan ba wani abu ba ne a wurinku, dukanku masu wucewa?

Ku duba ku gani.

Ko akwai wata wahala kamar

irin wadda nake sha,

wadda Ubangiji ya auko mini

a cikin zafin fushinsa?

13 "Daga sama ya aiko da wuta,

ya aiko ta cikin ƙasusuwana.

Ya shimfiɗa raga a ƙafafuna

ya juyo da ni.

Ya bar ni ni kaɗai,

sumamme dukan yini.

14 "Ya ɗaura zunubaina a wuyana;

aka naɗe su a hannuwansa.

Aka rataye su a wuyana

Ubangiji ya kwashe ƙarfina.

Ya bashe ni

ga waɗanda suka fi ni ƙarfi.

15 "Ubangiji ya ƙi

duk mayaƙan da suke tare da ni;

ya sa wata runduna ta tayar mini

ta kuma tattake samarina.

Ubangiji ya tattake budurwa Diyar Yahuda

kamar ’ya’yan inabi a wurin matsewa.

16 "Dalilin da ya sa nake kuka ke nan

idanuna kuma suna ta zubar da hawaye.

Babu wani a kusa da zai yi mini ta’aziyya,

ba wanda zai sabunta ruhuna.

’Ya’yana sun zama fakirai

domin maƙiyina ya yi nasara."

17 Sihiyona ta miƙa hannunta,

amma ba wani da zai yi mata ta’aziyya.

Ubangiji ya umarta cewa

maƙwabtansa za su zama maƙiyansa;

Urushalima ta zama

abar ƙyama a cikinsu.

18 "Ubangiji mai adalci ne,

duk da haka na yi tawaye da umarninsa.

Ku saurara, jama’a duka;

ku dubi wahalar da nake sha.

Samarina da ’yan matana

duka sun tafi bauta.

19 "Na kira abokaina

amma sun yashe ni.

Firistocina da dattawana

sun hallaka a cikin birnin

yayinda suke neman abinci

don kada su mutu da yunwa.

20 "Duba, Ubangiji, ka ga ƙuncin da nake ciki!

Ina shan azaba a raina,

ba ni da kwanciyar rai a cikin zuciyata,

domin na yi tawaye sosai.

A waje takobi na kisa;

a ciki kuma akwai mutuwa.

21 "Mutane suna ji ina nishi da ƙyar,

amma ba wanda zai yi mini ta’aziyya.

Dukan maƙiyana sun ji wahalar da nake ciki;

suna farin ciki da abin da ka yi.

Ka kawo ranan nan da ka sanar

domin su ma su zama kamar ni.

22 "Bari ka ga muguntarsu duka;

ka yi musu

yadda ka yi mini

domin dukan zunubansu.

Nishina da yawa

kuma zuciyata ta gaji."

Veja também

Publicidade
Lamentações
Ver todos os capítulos de Lamentações
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-