Publicidade

Lamentações 2

1 Yadda Ubangiji ya rufe Diyar Sihiyona

da gizagizan fushi! cikin fushinsa / ya yi da Diyar Sihiyona da wargi

Ya jefar da darajar Isra’ila

daga sama zuwa ƙasa;

bai tuna da wurin ɗora ƙafafunsa ba

a ranar fushinsa.

2 Ubangiji ya hallakar

da wurin zaman Yaƙub ba tausayi;

A cikin fushinsa kuma zai rurrushe

kagaran Diyar Yahuda.

Ya ƙasƙantar da mulki

da masu mulki.

3 A cikin zafin fushi ya fasa

kowane ƙaho na Isra’ila.

Ya janye hannun damansa

sa’ad da maƙiyi ya zo.

Ya yi ƙuna a cikin Yaƙub kamar wuta mai ƙone

duk abin da yake kusa da ita.

4 Kamar abokin gāba, ya ɗana bakansa;

hannun damansa na shirye.

Kamar maƙiyi,

ya kashe duk wanda idonsa ya ji daɗin gani;

ya zuba fushinsa kamar wuta

a kan tenti na Diyar Sihiyona.

5 Ubangiji kamar maƙiyi ne;

ya hallaka Isra’ila.

Ya hallaka wurarenta duka

ya kuma hallaka kagaranta.

Ya ƙara yawan makoki da baƙin ciki

wa Diyar Yahuda.

6 Ya rushe haikalinsa kamar lambu;

ya hallaka wurin yi masa sujada.

Ubangiji ya sa Sihiyona ta manta

da bukukkuwanta da kuma ranakunta na Asabbaci;

a cikin zafin fushinsa

ya watsar da sarki da firist.

7 Ubangiji ya ƙi bagadensa

ya kuma yi wofi da haikalinsa.

Ya ba maƙiyinta fadodinta;

suka yi sowa a cikin gidan Ubangiji

kamar a ranar da ake yin biki.

8 Ubangiji ya ƙuduri niyya yă rushe bangon

da yake kewaye da Diyar Sihiyona.

Ya auna da igiyar awo

bai fasa hallaka ta ba.

Ya sa katanga da katanga

duk suka lalace.

9 Ƙofofinta sun nutse a cikin ƙasa;

ya kakkarya ƙarafanta.

Sarakunanta da ’ya’yan sarakunanta

duk an kai su bauta cikin waɗansu ƙasashe,

babu sauran doka,

annabawa kuma ba su samun

wahayi daga wurin Ubangiji.

10 Dattawan Diyar Sihiyona

sun zauna shiru a ƙasa;

suka kuma sa rigar buhu.

’Yan matan Urushalima suka

sunkuyar da kawunansu ƙasa.

11 Idanuna sun dushe don yawan kuka,

raina na cike da baƙin ciki;

zuciyata ta karaya

domin mutanena sun hallaka,

domin yara da jarirai suna suma

a kan hanyoyi a cikin birni.

12 Suna ce wa uwayensu,

"Ina burodi da ruwan inabi?"

Yayinda suke suma kamar mutanen

da aka ji masu ciwo a cikin birni,

sa’ad da suke mutuwa

a hannuwan uwayensu.

13 Me zan ce miki?

Da me zan kwatanta ki,

ke Diyar Urushalima?

Da me zan misalta ki,

yadda zan iya yi miki ta’aziyya,

Ke Budurwa Diyar Sihiyona?

Ciwonki yana da zurfi kamar teku.

Wane ne zai iya warkar da ke?

14 Wahayin annabawanki

ƙarya ne kuma marasa amfani;

ba su tona zunubanki ba

yadda za su iya ceto ki daga bauta ba.

Sun yi miki annabcin ƙarya

marar amfani.

15 Duk masu wucewa

suna yi miki tafi na reni;

suna yi wa Diyar Urushalima

tsaki suna kaɗa kai suna cewa,

"Wannan ne birnin da aka ce

kyakkyawa ne,

mai farantawa dukan duniya rai?"

16 Maƙiyanki duka suna ta surutu

game da ke;

suna tsaki suna cizon haƙora

suna cewa, "Mun hallaka ta.

Wannan ce ranar da muke jira;

yau mun gan ta."

17 Ubangiji ya yi abin da ya shirya;

ya cika maganarsa,

wadda ya umarta tun daɗewa.

Ya jefar da ke ba tausayi,

ya bari maƙiya sun yi nasara da ke,

ya ɗaukaka ƙahon maƙiyanki.

18 Zuciyar mutane

ta yi kuka ga Ubangiji.

Ya bangon Diyar Urushalima,

bar hawayenki su zuba kamar rafi

dare da rana;

kada ki huta,

kada idanunki su huta.

19 Ki tashi, ki yi kuka cikin dare,

dare na yi sai ki fara kuka;

kina buɗewa Ubangiji zuciyarki.

Ki ɗaga hannuwanki gare shi

domin rayukan ’ya’yanki,

waɗanda suka suma don yunwa

a kan kowane titi.

20 "Ka duba, ka gani ya Ubangiji.

Wane ne ka taɓa yi wa haka?

Ko ya kamata uwaye su ci ’ya’yansu,

’ya’yan da suka yi reno?

Ko ya kamata a kashe firistoci da annabawa

a cikin haikalin Ubangiji?

21 "Matasa da tsofaffi duk

suna kwanciya a cikin ƙurar tituna;

an karkashe matasa

da ’yan matana da takobi.

Ka kashe su a ranar fushinka;

ka kashe su ba tausayi.

22 "Kamar yadda kake yin gayyata a ranar biki,

haka kake kawo mini tsoro a kowane gefe.

A ranar fushin Ubangiji

ba mai tserewa ba wanda zai tsira;

maƙiyina ya kashe waɗanda na yi renonsu,

na kuma lura da su."

Veja também

Publicidade
Lamentações
Ver todos os capítulos de Lamentações
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_06-50-08-