Pular para o conteúdo
Publicidade

Habakkuk 1

1 Saƙon da annabi Habakkuk ya karɓa.

Habakkuk ya nuna damuwa

2 Har yaushe, ya Ubangiji, zan yi kukan neman taimako,

amma ka ƙi ji?

Ina kuka a gare ka saboda zalunci

amma ba ka ce ufam ba.

3 Me ya sa ka bari ina ta kallon rashin gaskiya?

Me ya sa kake barin abin da ba daidai ba?

Hallaka da tashin hankali suna a gabana;

ga rashin jituwa da faɗa ko’ina.

4 Saboda haka ba a bin doka,

shari’a kuma ba ta aiki.

Mugaye sun kewaye masu adalci

don a hana gaskiya yi aiki.

Amsar Ubangiji

5 "Ka dubi al’ummai, ka gani,

ka sha mamaki.

Ga shi zan yi wani abu a kwanakinka,

wanda ko ma an faɗa maka

ba za ka gaskata ba.

6 Zan da Babiloniyawa,1.6 Ko kuwa Kaldiyawa

waɗannan marasa hankali da kuma marasa tausayi; masu gajeren haƙuri,

waɗanda suke ratsa ko’ina a duniya

don su ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.

7 Suna da bantsoro da firgitarwa;

dokoki da ƙa’idodinsu ne

kawai suka sani.

8 Dawakansu sun fi damisoshi sauri,

sun fi kyarketan yamma zafin rai.

Mahayansu suna zuwa a guje;

mahayansu daga nesa suka fito.

Suna firiya kamar ungulu mai sauka da gaggawa don ci mushe;

9 duk sukan zo da nufin tā-da-na-zaune-tsaye.

Ana jin tsoronsu tun ma kafin su iso

suna tattara bayi kamar yashi.

10 Sukan yi wa sarakuna ba’a

su kuma rena masu mulki.

Sukan yi wa dukan birane masu mafaka dariya;

sukan tara ƙasa su hau, su cinye abokan gābansu da yaƙi.

11 Sa’an nan su wuce da sauri kamar iska,

mutane ne masu laifi, waɗanda ƙarfinsu shi ne allahnsu."

Damuwa ta biyu ta Habakkuk

12 Ya Ubangiji, ba tun fil azal kake ba?

Ya Allahna, Mai Tsarkina, ba za mu mutu ba.

Ya Ubangiji ka sanya su su tabbatar da hukunci;

Ya Dutse, ka naɗa su don su yi hukunci.

13 Idanunka masu tsarki ne da suka fi gaban duban mugunta;

ba ka amince da abin da ke ba daidai ba.

To, don me ka ƙyale munafukai suna cin karensu ba babbaka?

Me ya sa kake shiru sa’ad da mugaye

suke haɗiye adalai da suka fi su adalci?

14 Ka mai da maza kamar kifin teku,

kamar halittun tekun da ba su da shugaba.

15 Mugu abokin gāba yakan kama su duka da ƙugiya,

jawo su waje da abin kamun kifinsa,

tattara su cikin ragarsa,

ta haka yakan yi murna da farin ciki.

16 Saboda haka yakan yi hadaya wa abin kamun kifinsa

kuma ƙona turare wa ragarsa,

domin ta wurin abin kamun kifinsa ne yake yin rayuwar jin daɗi

kuma zaɓi irin abincin da yake so.

17 Zai ci gaba da juye abin kamun kifinsu ke nan,

suna hallaka al’ummai ba tausayi?

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também

Habacuque
Ver todos os capítulos de Habacuque