Publicidade

Salmos 54

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Zifawa suka tafi wurin Shawulu suka ce, "Ba Dawuda ba ne yake ɓuya a cikinmu?"

1 Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka;

ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka.

2 Ka ji addu’ata, ya Allah;

ka saurari maganar bakina.

3 Baƙi suna kawo mini hari;

mutane marasa imani suna neman raina,

mutanen da ba sa tsoron Allah. Sela

4 Tabbatacce Allah ne mai taimakona,

Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni.

5 Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina;

cikin amincinka ka hallaka su.

6 Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka;

zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau.

7 Gama ya cece ni daga dukan wahalolina,

idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-