Publicidade

Salmos 126

Waƙar haurawa.

1 Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona,

mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.

2 Bakunanmu sun cika da dariya,

harsunanmu da waƙoƙin farin ciki.

Sai ana faɗi a cikin al’ummai,

"Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu."

3 Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu,

mun kuwa cika da farin ciki.

4 Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji

kamar rafuffuka a Negeb.

5 Waɗanda suka yi shuka da hawaye

za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.

6 Shi da ya fita yana kuka,

riƙe da iri don shuki,

zai dawo da waƙoƙin farin ciki,

ɗauke da dammuna.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-