Publicidade

Salmos 110

Ta Dawuda. Zabura ce.

1 Ubangiji ya ce wa Ubangijina,

"Zauna a hannun damana,

sai na sa abokan gābanka

su zama matashin sawunka."

2 Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyona

za ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka.

3 Rundunarka za su so yin yaƙi

a ranarka ta yaƙi.

Saye cikin ɗaukaka mai tsarki,

daga cikin ciki na safiya

za ka karɓi raɓar ƙuruciyarka.

4 Ubangiji ya rantse

ba zai kuma canja zuciyarsa ba,

"Kai firist ne har abada,

bisa ga tsarin Melkizedek."

5 Ubangiji yana a hannun damanka;

zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa.

6 Zai hukunta al’ummai, yana tarawa gawawwaki

yana kuma murƙushe masu mulkin dukan duniya.

7 Zai sha daga rafin da yake kusa da hanya;

saboda haka zai ɗaga kansa sama.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_06-50-08-