Publicidade

Salmos 87

Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Waƙa ce.

1 Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki.

2 Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona

fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub.

3 Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke

Ya birnin Allah, Sela

4 "Zan lissafta Rahab

a cikin waɗanda suka san ni,

Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush,

zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ "

5 Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce,

"Wannan da wancan an haifa a cikinta,

Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta."

6 Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa,

"An haifi wannan a Sihiyona." Sela

7 Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera,

"Dukan maɓulɓulaina suna cikinki."

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_18-40-07-