Publicidade

Salmos 70

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Roƙo.

1 Ka hanzarta, ya Allah, ka cece ni;

Ya Ubangiji, zo da sauri ka taimake ni.

2 Bari masu neman raina

su sha kunya su kuma rikice;

bari dukan masu sha’awar gani lalacewata

su juye baya da kunya.

3 Bari masu ce mini, "Allah yă ƙara!"

Su juye baya saboda kunyansu.

4 Amma bari dukan masu nemanka

su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka;

bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce,

"Bari Allah yă sami ɗaukaka!"

5 Duk da haka ni matalauci ne da kuma mai bukata;

ka zo da sauri gare ni, ya Allah.

Kai ne mai taimakona da mai cetona;

Ya Ubangiji, kada ka yi jinkiri.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_06-50-08-